A wannan makon za mu kawo muku ci gaba da hirar da Wakiliyarmu RABI’AT SIDI BALA ta yi daya daga cikin masu shirya fina-finan Hausa kuma Jarumi me taka rawa a cikin masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood wato MUDASSIR ISYAKU D.T.M, Jarumin da ke taka rawa cikin fina-finan da ke haskawa a yanzu, Jarumin ya bayyana babban kalubalen daya fuskanta bayan shigarsa cikin masana’antar Kannywood, baya ga haka Jarumin yayi karin haske ga masu kallo da masoyansu, dangane da irin rashin lokutan da sauran Jarumai ke rasawa yayin da suke bukatarsu, tare da kira ga gwamnati wajen magance matsalolin da ke afkuwa a cikin masana’antar, har ma da wasu batutuwan masu yawa. Ga dai yadda tattaunawar ta kasance:
Ci gaba daga makon jiya
Wacce irin mace kake son aura?
Ina son fara, doguwa, kyakkyawa, barumaya me tsagar ‘eleben’ ‘yar Katsina ko kuma me bille sillubawa, in ba ta samu ba, ina son fara kyakkyawa me addini, me riko da addini, sannn wadda take sona tsakani da Allah, ita nake son aura.
Kamar yaushe kake sa ran yin aure?
Nan da bayan Sallah babba, In Allah ya yarda.
Wanne kira za ka yi ga masu kokarin shiga masana’antar kannywood har ma da wadanda suke ciki?
Kiran da zan yi ga masu son shiga harkar fim, na farko dai in za ka shiga harkar fim ka tabbatar ka samu amincewar iyayenka, uwa ko uba ko kuma dukkansu in suna raye, domin yardarsu shi ne za ka samu nasarori, sannan abin da ka je yi za ka samu. Addu’arsu za ta kai ka ga inda baka tunani. Wanda suke ciki kuma duk abin da mutum zai yi, ya yi shj sabida Allah, sannan ina kira ga wasu daraktoci ko furodusas in wani ya zo yana so zai shiga namiji ko mace ko ma wane ne, in kana da dama ka bashi shawara yadda zai fara ya shiga dan taiyu, sai ya zo ya shiga kai kana ciki shekara da shekaru amma ya zo Allah ya bashi wani nasibi wanda kai ba ka da shi, Allah ya bashi daukakar da kai ma sai ka nemi wani abu a tattare da shi, dan haka idan har ka yi mu’amulla ta gaskiya da shi, ka fada masa gaskiyar yadda ya kamata yayi, toh kai ma Allah zai duba ka. Sannan su rike sana’arsu, su rike mutuncinsu, har kar fim sana’a ce me mahimmanci, sannan harkar fim sana’a ce me nasibi da yawa a cikinta.
Wanne sako kake da shi ga masu kallo har ma da masoyanka?
Sakona ga masoya da masu kallon fina-finanmu ina so dan Allah idan dan fim yayi wani abu a rinkai masa uzuri, sannan idan masoyi ya kiraho ka, ko ya nemi yin mu’amulla da kai ko wani abu, wani lokacin abubuwa suna yi mana yawa,dan wallahi akwai lokacin da in ta kacame kana aiki, wallahi ni akwai lokacin da na sha ruwa ‘pure water’ ne, ledar ‘pure water’ na sata a cikin aljihu. Yanzu a daidai wannan lokacin masoyi ko wani me kallo zai iya kiranka kuma ya ce dole sai ka saurare shi, toh a rinka yin uzuri, yadda kake son shi din nan kuma daga wani gari ko a garinka ko a unguwarku, ko a ina ne, toh shi fa wannan harkar da ya ke ta fim din nan akwai su a kowacce Jiha irin wadannan, akwai su kuma a wasu kasashen. Toh! za ka ga abubuwa suna yi musu yawa, toh sai ana yi musu uzuri, dan Allah a rinwa yi musu uzuri, kuma masoya muna godiya, sabida sai da ku in ba kwa yi ko kuma ba kwa kalla toh muma ba za mu yi ba, kuma ba za mu ji dadi ba, duk abin da muke yi muna son masoya. In mun yi kuskure kuma a gaya mana kuskure mu, inda kuma muka yi daidai nan ma a yaba dan mu samu kwarin gwiwa, kuma da samun danar yin wani abun, wanda ya fi wannan.
Ko akwai wani kira da za ka yi ga gwamnati game da ci gaban masana’antar Kannywood?
Kiran da zan yi ga gwamnati sai dai na ce mun gode, Allah ya saka da alkhairi, sannan a kara inganta mana harkar sana’ar mu, domin sana’ar fim waje ne daya tara mutane daban-daban, bana mantawa shekara 4 da suka huce an kulle duk wanda zai shigo sai yayi ‘register’, kuma kowa yayi mabambantan ma’aikata duk na ‘industry’ kama daga kan ‘camera man, diector, producer, sound’, mawaka dukka kowa yayi wannan ‘register’. Toh! ya kamata a ce duk wanda ya ke da irin wannan ‘register’ gwamnati muna kira a gare ta ta zo ta shigo ciki ta tallafa. Mun gode shawagabanninmu da suka sassamu Allah ya sa su zamar mana mafi alkhairi, Allah ya kaho mana saukin rayuwa.
Wanne irin abinci, da abun sha ka fi so?
Abincin dana fi so Shinkafa da wake da mai da yaji shi ne ‘best food’ dina, abin da kuma na fi so na sha, ina son Fura irin ta Katsina ba wai dan garinmu bane ba fa, Furar Katsina akwai dadi sosai, sannan a lemo irin ‘drinks’ haka lemon dana fi so shi ne Miranda da ‘Apple’.
Me za ka ce da makaranta wannan shafin na Rumbun Nishadi?
Masu bibiyar wannan shafi na Rumbun nishadi, sai na ce su ci gaba da bibiyar shafin kamar yadda kuka saba, Jaridar Leadership taku ce ta mu ce, ni ma tawa ce.
Me za ka ce da ita kanta jaridar LEADERSHIP Hausa?
Ina godiya sosai da wannan jarida ta LEADERSHIP wadda ta hanga ta hango ni har ta zakulo ni a cikin masana’antar Kannywood tayi hira da ni, muka tattauna har na tsahon awa biyu kenan, muna wannan hira. Babu abin da zan ce sai dai na ce Allah ya saka musu da alkhairi, Allah kuma ya kara daukaka wannan jarida na gode na gode sosai, ba zan taba mantawa da ita ba.
Ko kana da wadanda za ka gaisar?
Ina gaida maigidana Ali Rabi’u Ali Daddy da mataimakinsa Ghali Ibrahim ‘Yan Doya, Mas’ud MMCD, da Isma’il Khalil Ja’en da kuma uwata a ‘industry’ Hajiya Zahra’u Sale Fantami wato Adaman Kamaye, ina gaishe su, ina gaishesu sosai, da duk sauran daraktocinmu, da furodusas dinmu, da marubutanmu, da kowa da kowa.
Muna godiya ka huta lafiya
Ni ma na gode.