Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta jaddada cewa, sam bai dace ba a bayyana adawa da ballewar Taiwan a matsayin abun da zai sauya halin da ake ciki a mashigin tekun Taiwan.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin, Wang Wenbin ne ya bayyana haka, lokacin da aka yi masa tambaya kan tsokacin da kungiyar G7 ta yi a baya-bayan nan dangane da batun Taiwan.
A jiya Lahadi ne ministocin harkokin wajen kasashe mambobin kungiyar G7 suka yi taro a garin yawon shakatawa na Karuizawa na yankin Nagano dake kasar Japan. Kuma yayin taron, kasahen G7 sun amince cewa, dukkansu na adawa da sauya halin da ake ciki a zirin Taiwan ta karfi tare da jaddada muhimmancin zaman lafiya da kwanciyar hankali a zirin.
A martaninsa, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Wang Wenbin, ya bayyana cewa, idan har an damu da yanayin da ake ciki a zirin Taiwan, to kamata ya yi a lalubo musababbin abun da ya haifar da zaman dar dar a yankin.
Ya ce hujjoji sun nuna cewa, masu neman ‘yancin Taiwan da hadin gwiwa da taimakon wasu daga kasashen waje, na yin dukkan mai yiwuwa don taimakawa ayyukan neman ballewar yankin, wanda ke lalata yanayin da ake ciki a zirin Taiwan, haka kuma shi ne musababbin zaman dar dar a zirin. (Fa’iza)