Ma’aikatan filin jiragen saman Jihar Legas, sun fara yajin aikin gargadi na kwanaki biyu daga ranar Litinin bayan cikar wa’adin sanarwar kwanaki 14 da suka yiwa Ministan Sufuri.
Dalilan da suka haifar da wannan yajin aiki na gargadi da ma’aikatan suke yi sun hada da rashin bayyana sabon tsarin aikinsu wanda aka yi tun shekaru bakwai da suka gabata da kuma batun rushe ofishinsu da ke Legas.
- Za A Kammala Titin Kaduna Zuwa Kano Kafin Buhari Ya Sauka —Fashola
- Ramadan: Lokutan Sahur Da Buda-baki Na Azumi Na 27
Ma’aikatan sun fara yajin aiki a bisa dalilin rashin tabbatar da sabon tsarin aikinsu da kamfanonin jirage hudu suka yi tun shekaru bajwai da suka gabata.
Ma’aikatan sun sanya shinge a kan hanyar shiga cikin filin jirgin ta barin matafiyan cikin gida a filin jirgin saman Murtala Muhammad da ke Lagas, matakin da ya dakatar da dukkanin harkoki a filin.
Tun farko dai ma’aikatan sun bada sanarwar shiga yajin aikin kwanaki biyu a ranar Lahadi.
Wannan mataki ya sanya damuwa a zukatan kamfanonin jiragen sama musamman na bangaren yadda zai shafi hada-hadar harkokin fasinjoji lamarin da ya sa wasu cikinsu suka fara tuntunbar shugabannin kungiyoyin ma’aikatan domin kawo karshen sabanin.
Tun a makon da ya gabata, kungiyoyin ma’aikatan suka sanar da mambobinsu a game da shirin da suke yi na shiga yajin aiki na gargadi tsakanin ranar ranar Litinin da kuma ranar Talata, sannan idan har ba a biya musu bukatunsu ba, za su zarce har sai baba ta gani.
Kungiyoyin ma’aikatan jiragen sama biyar ne suka shiga yajin aikin; kuma sun hada da NUATE kungiyar ma’aikatan sifirin jiragen sama ta kasa, sannan akwai kungiyar manyan ma’aikatan harkokin zirga-zirgar jirage ta Nijeriya (ATSSSAN), kungiyar Nijeriya na kwararun ma’aikatan zirga-zirgar jiragen sama (ANAP) da kuma kungiyar matuka jiragen sama da injiniyoyi ta Nijeriya da kuma gamayyar kungiyar ma’aikatan gwamnati da ma’aikatan nishadi ta kasa.
Ma’aikatan sun ce tun farko sun bai wa Ministan sufuri sanarwar kwanaki 14 a ranar 7 ga watan Fabrairu na wannan shekara amma ba a dauki wani mataki ba har sai da wa’adin da suka ba shi ya shude.
Kungiyoyin ma’aikatan suna korafi a game da rashin aiwatar da karin albashin da aka musu da kuma lissafin da ya hau bayan da aka yi wa albashin hukumar NIMET kwaskwarima tun daga 2019 da kuma kin amincewa da fitar da sabon tsarin aikinsu da hukumar albashi na kasa (NSIWC) da kuma ofishin shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya (OHCSF) suka ki yi.
Ma’aikatan sufurin jiragen sama sun kaddamar da zanga-zanga a birnin Legas inda rahotanni suke bayyana cewa, hukumomin tsaro sun kama wani dan jarida mai daukar hoto bisa dalilin cewa, ya hallarci zanga-zangar dan gudanar da aikinsa.