Da safiyar yau Talata aka kaddamar da bikin haduwar matasan Sin da Afirka karo na 7 mai taken “yin kokari tare don cimma burin matasa da raya hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka” a nan birnin Beijing.
Wakilin Sin na musamman mai kula da harkokin Afirka Liu Yuxi ya bayyana a gun bikin budewar cewa, yayin da ake fuskantar yanayin duniya maras tabbaci, ya kamata matasan Sin da Afirka su girmama mabanbantan al’adun kasa da kasa, da tabbatar da adalci da koyi da juna da yin shawarwari da amincewa da bambance-bambance a fannnin al’adu, kana su yi kokarin neman samun zaman lafiya, da bunkasuwa, da adalci, da demokuradiyya, da ‘yanci, kuma su gujewa nunawa juna kiyayya domin bambancin ra’ayoyi, kana su hada hannu wajen tinkarar kalubalen duniya daban daban tare.
Jakadan kasar Senegal dake kasar Sin Ibrahima Sory Sylla ya bayyana cewa, bangaren Afirka na yabawa kasar Sin domin ta nuna goyon baya ga aikin bada ilmi da horar da kwararru a nahiyar Afirka, kuma ya kamata Afirka da Sin su ci gaba da yin hadin gwiwa da juna a wannan fanni don kara samar da dama ga matasan bangarorin biyu. (Zainab)