A yau Laraba ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya zanta da takwaransa na kasar Gabon Ali Bongo Ondimba, wanda ke ziyarar aiki a kasar Sin. Yayin tattaunawar tasu, shugaba Xi ya ambaci shugaba Bongo da “Dadadden aboki” na al’ummar kasar Sin, yana mai cewa, shugaban na Gabon, shi ne shugaban wata kasa daga nahiyar Afirka na farko, da ya karbi bakuncin sa, tun bayan sake zabar sa a matsayin shugaban kasar Sin, wanda hakan ke tabbatar da muhimmanci, da babban matsayin alakar Sin da Gabon.
Shugaba Xi ya kara da cewa, a matsayin ta na aminiyar Gabon, Sin na yiwa Gabon din fatan samun gagarumin ci gaba a dukkanin sassan, tare da tabbatar da burin ta na cimma dabarun bunkasa Gabon mai tasowa.
Ya ce karfi da dorewar ci gaban dangantakar sassan biyu, su ne suka haifar da gajiyar da kasashen biyu ke ci daga juna, kuma hakan ya zamo abun misali a fannin gina al’umma mai makomar bai daya ga daukacin bil adama.
Daga nan sai shugaban na Sin, ya gabatar da shawarar daga matsayin cikakkiyar dangantakar hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu, zuwa cikakkiyar dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare. (Saminu Alhassan)