ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hare-haren Bindiga Da Ke Hallaka Amurkawa Na Shaida Gazawar Gwamnati Wajen Kare Hakkin Bil Adama

by CMG Hausa
3 years ago
Bindiga

Abokai, a karshen makon da ya gabata, fararen hular kasar Amurka sun sha fama da harbe-harben bindiga, wanda hakan ya haifar da asarar rayuka da dama. Bisa labarin da aka bayar, a daren ranar 15 ga watan nan, an samu aukuwar harin bindiga a garin Dadeville na gabashin jihar Alabama, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane a kalla 4, baya ga sauran wasu 28 da suka ji rauni.

Baya ga haka, a wannan rana, an fuskanci hare-haren bindiga a wata jami’a dake kudu maso gabashin jihar Pennsylvania, da wani lambun shan iska dake birnin Louisville na jihar Kentucky, hare-haren da suka yi sanadin mutuwar mutane 2 da jikkatar wasu 4.

  • Matsakaiciyar Karuwar Sana’ ar Manhajoji A Sin Ta Kai Kaso 16% Duk Shekara

Bisa kididdigar da shafin intanet na Gun Violence Archive ya bayar, tun farkon wannan shekara zuwa yanzu, an samu aukuwar hare-haren bindiga a wuraren da jama’a ke taruwa har sau 163, lamarin da ya haifar da rasuwar mutane fiye da dubu 12.

ADVERTISEMENT

A hannu guda kuma, kungiyar masu rajin kare mallakar bindiga ta Amurka ta NRA, ta gudanar da taron shekara-shekara a ran 14 ga watan nan, a birnin Indianapolis na jihar Indiana, bikin da masu goyon bayan mallakar bindiga da dama suka halarta, ciki har da wasu manyan jami’an jam’iyyar Republican wadanda suka bayyana goyon bayansu ga NRA.

A daya bangaren kuma, cibiyar dake rajin kare dokar hana hare-haren bindiga ta Giffords dake kasar Amurka, ta fitar da rahoto dake cewa, NRA mai mambobi fiye da miliyan 5 da kudade masu dimbin yawa, na da babbar alaka da harkokin siyasa da suka shafi zabuka a kasar, kuma hakan ya sa ‘yan siyasa ke dora muhimmanci sosai a kan kungiyar.

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cibiyar ta kara da cewa, yayin da ‘yan siyasar Amurka ke ja-in-ja da juna kan batun mallakar bingida, fararen hula ne kawai suke daukar asara.

Gwamnatin Amurka wadda ake jinjinawa da sunan “Mai kare hakkin Bil Adama”, mutuncinta ya zube, sakamakon yawan aukuwar hare-haren bindiga dake addabar al’ummar kasar. (Mai zane da rubuta: MINA)

Bindiga
CMG Hausa
+ postsBio
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Shugabannin Kasashen Duniya Sun Yi Wa Sin Fatan Alheri A Sabuwar Shekara
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    San Francisco sabon mafarin hadin gwiwar Sin da Amurka ne
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Xi Ya Halarci Kwaya-Kwaryan Taron Shugabannin Mambobin APEC
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Shugaban Kasar Sin Ya Gabatar Da Rubutaccen Jawabi Ga Taron Jagororin Masana’antu Da Kasuwanci Na APEC

MASU ALAKA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
Daga Birnin Sin

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
Daga Birnin Sin

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
Daga Birnin Sin

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Next Post
Karamar Sallah: Gwamnatin Tarayya Ta Ba Da Hutun Ranar 21 Da 24 Ga Afrilu

Karamar Sallah: Gwamnatin Tarayya Ta Ba Da Hutun Ranar 21 Da 24 Ga Afrilu

LABARAI MASU NASABA

Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.