An rufe zangon farko na bikin baje kolin kayayyakin shige da fice na kasar Sin wato Canton Fair karo na 133 a jiya Laraba. An gudanar da bikin na wannan karon a zahiri, inda ya kasance mafi girma a tarihinsa.
Ya zuwa jiya, jigilar mutanen da suka isa wajen bikin ya kai fiye da miliyan 1.26. A cikin masu sayayya na ketare, kusan daya bisa biyar sun fito daga kasashen Afirka da yammacin Asiya.
A cikin ’yan shekarun baya, hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka da na yammacin Asiya ya sami gagarumin ci gaba a fannonin tattalin arzikin zamani da neman ci gaba maras gurbata muhalli, da hada-hadar kudi da sararin samaniya da dai sauransu. Kawo yanzu, Sin ta zama daya daga cikin kasashe 4 da suka zuba mafi yawan jari a kasashen Afirka. Sannan kasashen yammacin Asiya da na Afirka da dama, su ma sun zuba makudan jari a wasu muhimman ayyuka na kasar Sin. (Safiyah Ma)