Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aika sakon murnar cika shekaru 100 da kafa jami’ar Yunnan, inda ya isar da gaisuwa da fatan alheri ga daukacin malamai da daliban jami’ar.
A cikin sakonsa, Xi ya yi nuni da cewa, a cikin shekaru 100 da suka gabata, jami’ar Yunnan ta horar da fitattun kwararru da yawan gaske, wadanda suka taka babbar rawa kan hada kan kalibu daban daban da ci gaban tattalin arzikin kasar Sin.
An kafa jami’ar Yunnan ne a shekarar 1922, inda ta kasance daya daga cikin hadaddun jami’o’in da aka kafa a iyakar kasa dake yammacin kasar Sin. (Mai fassarawa: Jamila)
Talla