Assalamu Alaikumu masu karatu barkammu da sake haduwa a cikin shirin namu mai farin jini da albarka na ado da kwalliya.
A lokacin azumi zakiga gida ya yi datti saboda ba lokacin gyaran gida so sai duba da yanayin azumi yanada aiki sannan kuma ga ibada kamar tashin dare, da safe zaki ga kindan koma kafin ki tashi ki danyi share share yadda kika saba zakiga lokaci ya tafi ga kuma shiga kicin da wuri shine yake sawa be,a samun damar gyara gida kamar yadda ya kamata sannan kasan cewar gida da azumi da kuma lokacin sallah yana kaca kaca saboda aikin azumi dana sallah, sai an gyara shi bayan sallah.
- Da Dumi-Dumi: Sarkin Musulmi Ya Ayyana Juma’a A Matsayin Ranar Sallah
- Bunkasuwar Kasar Sin Mai Inganci Ta Ingiza Kwarewar Jama’arta
To yau za mu san yadda ake gara gidan bayan sallah.Da farko Uwargida za ki kwashe kayan kicin dukkwanikanki da yake cikin kicin din da wani tarkacammu na bata, gaba daya sai ki sake wanke su gaba daya kayan kicin din, ki shanyasu saboda su bushe, sannan sai ki wanke kicin din har bango ki kada ruwan omo da dan hypo saboda kwari kisa soso idan kika wanke bangon dama kin tanaji dan tawul haka sai kibi ki goge kumfar zakiga yadda tayis ( tiles) din bangon kicin dinki yake shayinin abin sha,awa saman inda tsayinki bazai kaiba sai kisa mopper kinabi kina gogewa za kiga duk wani maikon girki kin gogeshi idan kika gama goggoge bangon kicin din sai ki wanke gas dinki so sai ciki da waje ki gogeshi, sai ki shigo da kwanikanki ki maidasu kinsan kingama da kicin. Sai falo za ki fara da windo ki kakkadeshi sannan ki hada ruwan omo kisamu gyalle haka ki goggogeshi zakiga ya yi haske duka windonan haka za ki musu, sannan kujeru sai ki jajjanye su ki kakkade su ki share kasan su sai ki mayar su idan kinaso sai ki juyasu yadda ki kaga zasuyi kyau sannan sai ki share falon ki, ki goggoge TB dade sauransu, yadda kika yi windon falo haka za kiyi na daki, sai ki daga gadon shima ki kakkade sannan ki share kasan gadon ki mofe ki maidashi yadda kike so, Sai ki wawwanke bandakin ki so sai zakiga gidanki ya yi kyau so sai har wata iska mai dadi zaki ji tana shigowa. Duk wani dattin da ya makale na azumi da aikin sallah idan kikayi haka zai fita gaba dayan su.