A daidai lokacin da al’ummar Musulmi ke shiga shagulgulan sallah, mutane a Nijeriya na kokawa da yadda al’amura suka sauya, musamman yadda rayuwa ta yin tsanani ta yadda mafi yawan magidanta suke shan wahala wajen ciyar da idalansu sakamakon matsalar tsaro, karancin kudi da kuma tsadar rayuwa a tsakanin magidanta.
Galibi idan aka kawo karshen azumin watan Ramadan, musulmi na gudanar da bukukuwan sallah tare taya juna murna da fatan alkairi na kara ganin bikin wata shekara.
- INEC Ta Musanta Zargin Bangaranci A Zaben Adamawa
- Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Sabon Rigakafin Zazzabin Cizon Sauro
Bikin sallar ta bana ta zo ne a kan gaba ta yadda Nijeriya suka tsunduma cikin rashin tsaro da karancin kudi a hannun mutane da kuma tsadar rayuwa. Wadannan matsaloli sukan iya shafar tagomashin bikin sallan, domin mafi yawancin magidanta na kokawa kan matsin tattalin arziki wanda ya hana sayan kayayyaki da aka saba saya lokacin bukukuwan sallah.
Wasu kuma sun dage sai sun yi bikin salla a fili duk da cewa ba su da kudin sayan tufafi da kayan abinci da sauran kayan amfanin gida da za su sa bikin ya yi armashi.
Idan aka dauki tsadar rayuwa a nan za a iya cewa tuni dai farashin kayan masarufi dama sauran kayayyakin amfanin yau da kullum ya yi tashin goron zabi, abin da ya sa jama’a da dama suka shiga cikin kuncin rayuwa da halin lahaula. Kusan babu abun da bai kara kudi ba, kuma kullum farashin sauyawa yake yi, zai wahala ka je sayen abu a kasuwa yau, gobe ka koma bai kara kudi ba.
Matsalar Tsaro
Matsalar tsaro musamman a Arewacin Nijeriya na ci gaba da ta’azzara. Kusan kullum sai an sami rahoton kai sabon hari a wani yanki duk da jami’an tsaro suna samun nasarar dakile wasu hare-haren da kama maharan da masu safarar makamai su kai wa ‘yan ta’addan, amma lamrin ya ki ci ya ki cinyewa. Lamarin tsaro na haifar da babban cikas ga shagulgulan sallah, don al’umma suna zama cikin dar-dar da rashin kwanciyar hankali ta yadda ba su sami damar gunar da bukukuwan yadda ya kamata ba.
Sai dai al’umma sukan manta da cewa, tsaro aikin kowa ne kuma ya kamata mu dauke shi a haka har ma a fara daga gida. Idan kowa ya yi nazari zai gane cewa su fa wadannan ‘yan bindiga sun fito ne daga gida, tare da uwa da uba, ba su fado daga sama ba. Rashin tsaro da al’umma ke fama da shi a halin yanzu ya samo asali ne sakamakon sakaci da rashin kulawa da iyali a wurin magidanta.
Ya kamata gwamnati a dukkan matakai da su magance matsalar rashin tsaro a Nijeriya, don sannu a hankali matsalar tsaro yana lalata kasar nan ta kowacce fuska.
Sannan kuma kira ga ’yan siyasa da su yi kokari su fifita maslahar kasa fiye da kowa da kowa, su fuskanci wadannan matsalolin kwata-kwata kamar yadda suke fuskantar wakilan jam’iyya, dole ne a dauki al’amuran tsaro da matukar muhimmanci, sannan kuma a yi aiki da ilimi wajen dinke bakin zaran.
Karancin Kudi
Duk da cewa ana samun kudade a bankuna da sauran wuraren cire kudade daban-daban da ke fadin kasar nan, amma akwai karancin kudin a hannun mutane, kuma hakan ya zama cikas a bukukuwan Sallah. Sanin kowa ne ana bukatar kudi a hannu musamman don bai wa ‘yan yawon Sallah wadanda suke kai ziyara ga ‘yan’uwa da abokan arziki, inda hakan ke kara dankon zumunci. Rashin wadannan kudade a hannun mutane ya sanya wasu suka zauna a gida suka ki kai wannan ziyarar don sun saba idan sun kai ziyara sukan bayar da kudi ga ‘yan’uwa da abokan arziki, musamman ma kananan yara, a yayin da wasu kuma da a kan je wurinsu su gudu daga gidajensu ko an zo ba za a gansu ba don ba su da kudin da za su bayar idan an kawo masu ziyara kamar yadda aka saba.
Akwai bukatuwar gwamnati ta duba wannan lamarin da idon basira na wadata kudade a hannun jama’a, domin daukan matakin da ya dace. Idan gwamnati ta dauki wannan mataki hakan zai bunkasa tattalin arziki a kasa baki daya. Duk da cewa kasashen da suka ci gaba su suke da tsarin takaita kudi a hannu mutane, amma mu a halin yanzu ba mu kai ci gaban da za a aiwatar da wannan tsarin ba.
A baya dai, gwamnatin tarayya ta kaddamar da tsarin takaita kudade a hannun Nijeriya, wanda yakai ga sauya wasu takardun kudade domin samun damar takaita kudade a hannun mutane da kuma bankuna da ke fadin kasar nan.
Lamarin da ya sa dimbin jama’a suka kasa samun sabbin takardun kudi, kuma sun kasa siyan abubuwan da suke bukata. Wannan ya haifar da tabarbarewar tattalin arziki ba kamar guguwar Tsunami a fadin kasar, inda ta jawo wa ‘yan kasa wahalhalun da ba a taba ganin irinsa a Nijeriya.
Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya bayyana cewa, tsarin kayyade yawan kudade zai taimaka wajen dakile safarar kudaden haram da kuma bunkasa hada-hadar kudi ta hanyar zamani a Nijeriya. Sai dai tsarin maye gurbin tsoffin takardun kudin bai yi daidai da yadda ya kamata ba duba da irin matsalolin da ‘yan kasar ke fuskanta wajen samun sabbin takardun kudi.
Tsarin dai ya sa mutane muna kwana a bakin na’urar cire kudi ta ATM, domin samun kudaden gudanar da kasuwanci da kuma harkokin yau da kullum.
An danganta wannan lamari da yadda CBN bai buga isassun sabbin takardun kudi ba. Wannan ne ya haddasa isasshen kudi daga wurin bankunan kasuwanci, inda suka kasa wadata abokan kasuwancinsu wanda hakan ya sa aka samu karuwar mabuka. ‘Yan Nijeriya dai ba su ji da dadi ba kan wannan tsari.
Babban Bankin na son kafa tsarin mu’amalar kudi da ake yi ta hanyar intanet, amma bankuna ba su da ingantattun kayayyakin aiki da za su iya gudanar da tsarin. A lokacin kaddamar da wannan tsarin, an samu cinkoso a bankuna wajen musanya kudade bisa tsarin da gwamnatin tarayya ka zo da shi.
Gwamnati na cewa tsarin zai habaka tattalin arzikin Nijeriya. Yawancin masana tattalin arziki sun nuna shakkusu bisa hanyar da aka bi wajen aiwatar da tsarin. Inda suka bayyana cewa cin hanci da rashawa ya dade yana dabaibaye jami’an gwamnati wanda hakan ba zai taba bari tsarin ya tafi yadda ya kamata ba, kuma hakan ke kara haifar da wahalhalu ga dimbin masu fama da talauci a kasar nan.
A watan Oktoba na shekarar bara, sama da kashi 80% na naira tiriliyan 3.2 da ake yawo a Nijeriya na hannun ‘yan kasuwa, amma kashi 75% na kudin yanzu an ajiye su ne a cibiyoyin hada-hadar kudi, a cewar gwamnan Babban Bankin Nijeriya, Godwin Emefiele. Yayin da ‘yan Nijeriya da dama ke ajiye kudadansu a bankuna, wasu bankunan na ci gaba da tatsar abokan kasuwanci caji mai yawa a lokacin da suka zo cire kudi.
Hukumomin Nijeriya sun bayyana cewa daga cikin dalilan da ya sa aka sauya kudaden shi ne, takaita amfani da kudade wajen sayan kuri’a. sun ce hakan zai taikama wa talakawa. A cewarsu, ana yin amfani da kudade wajen sayan kuri’un talakawa.
Wannan lamari ya haddasa hauhawar farashin kayayyaki na 21.3.
Dukkan wadannan abubuwan sun jawo wahalhalu masu yawa a kauye da birane, wanda mutane suke ganin da gangan ne aka shigar da su. Karancin kudi ya yi illa ga kowane bangare na rayuwar ‘yan Nijeriya, amma abin da ya fi tayar da hankali shi ne, mutuwar da aka ruwaito sakamakon halin da mutane suka shiga wanda za a iya kauwa wa lamarin idan har aka kaddamar da tsarin yadda ya kamata.
Kafafen yada labarai sun ruwaito yadda ‘yan Nijeriya ke mutuwa a asibitoci saboda ba su da kudin da za su biya a asibiti sakamakon wannan tsarin. Wannan bai kamata ya zama abin mamaki ba ganin yadda akasarin ‘yan Nijeriya ke biyan kudi daga aljihunsu domin samun aikin jinya, sabanin yadda ake yi a sauran lokutan da inshorar lafiya na duniya ke sa wadanda suka yi rajista su samu aikin kiwon lafiya ba tare da neman kudi ba. Nijeriya dai kasa ce mai karfin tattalin arziki, amma tsarin da CBN ya bullo da shi ba zai harfar wa Nijeriya da mai ido ba.
Bayan karancin kudi, ‘yan Nijeriya na kokawa da karancin man fetur wanda kuma ya yi tasiri sakamakon karancin takardun naira.
‘Yan Nijeriya da dama a cikin birane ba sa iya siyan mai a gidajen mai, saboda gidajen man ba sa siyarwa ba tare da biyan tsabar kudi ba, kuma tsarin biyansu ta yanar gizo ba ya aiki. A mafi yawan sassan kasar nan ana sayar da man fetur sama da kashi 500, sama da farashin da gwamnati ta amince da shi na naira 180-185 kan kowace lita. Wadannan sun kara jefa talakawan Nijeriya cikin mawuyacin hali.
Tsadar Rayuwa
A yanzu haka rahotanni sun nuna cewa akwai mutanen da abin da za su kai bakinsu salati ma a kullum na matukar yi musu wahala bare a sami abubuwan da za a yi shagalin sallah da su. Ko da yake akwai masu ganin cewa, tun dai bayan rufe iyakokin Nijeriya da gwamnatin tarayya ta yi aka fara samun tashin farashin kayayakin abinci musamman shinkafa wacce ita ce babban abincin da aka fi amfani da shi a Nijeriya da dai makamantansu, wanda han ya haifar da tsadar rayuwa a cikin wannan kasa.
Amma a hannu guda kuwa, gwamnati ta bayar da bayanai a kan abubuwan da take gani sun haddasa tsadar rayuwa da kuma tashin farashin kayayyaki, inda take cewa karayar tattalin arziki da annobar cutar Korona ta jawo cikas ga kasashen duniya ta hanyar durkushe ayyukan hakar ma’adinai da ake amfani da su wajen wajen sarrafa taki, ma’ana akwai matsalar takin zamani ga manoma da rashin aikin yi ga ma’aikatan hako ma’adanai wanda hakan ta kara tasiri wurin ruruta wutar tsadar rayuwa a Nijeriya.
Hakan ya sa taki ya yi tsada ga noman rani har zuwa yanzu, ta yadda wadansu sun noma shinkafa sun rasa takin saka mata dole ta sa suka saida wa makiyaya shinkafar.
Akwai kuma karin farashin man fetur da na hasken wutar lantarkin da aka yi a Nijeriya sun sake jefa ‘yan Nijeriya a mawuyacin hali, kuma hakan ya shafi shagulgulan sallah.
Dangane da bayanan baya-bayan nan da Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta fitar, hauhawar farashin kaya a Nijeriya ya ragu kadan zuwa kashi 21.34 cikin dari a watan Disambar 2022, idan aka kwatanta da na watan Nuwamban 2022 wanda ya kai kashi 21.47 a duk shekara.
Dangane da hauhawar farashin kayan abinci, NBS ta ce: “Yawan hauhawar farashin kayan abinci a watan Disambar 2022 ya kai kashi 23.75 bisa 100, wanda ya kasance sama da kashi 6.38 idan aka kwatanta da adadin da aka samu a watan Disambar 2021 na kashi 17.37.” Wannan tashin farashin kayan abinci ya samo asali ne sakamakon hauhawar farashin biredi da hatsi, mai, dankali, dawa, kifi da sauran kayan abinci.
Wannan gwamnatin ta yi kokari wajen tabbatar da tsaro da sawo kan matsalolin tattalin arziki da kuma fatattakan latauci a tsakanin ‘yan Nijeriya.
Duk da kokarin gwamnati na sawo kan lamarin, rashin tsaro na kara yaduwa a fadin kasar nan. A daidai lokacin da mayakan ‘yan ta’addan Boko Haram a Arewa maso Gabas sun ci gana da zafafa hare-hare babu kakkautawa. Bugu da kari, wasu ‘yan bindiga na ci gaba da haddasa tarzoma ta hanyar yin garkuwa da mutane da kisan kiyashi a wasu sassan Zamfara da kuma mahaifar shugaban kasa wato Jihar Katsina.
Ana ci gaba da kai hare-hare da ramuwar gayya a jihohi kamar irin su Kaduna da dai sauransu, inda a kowacce rana sai an samu labarin kai hari a kudancin da arewacin jihar.
Yana da wuya a ce kullum sai an yi maka yadda kake so ko kuma ka sami abun da kake so, ko yanayi ya zo maka yadda kake fata, ko kuma sai ka ji abin da zai yi maka dadi, ko sai idonka ya ga abin da zai faranta maka rai musamman a bikin sallah wanda masu iya magana suke cewa, ‘Sallah biki daya rana,” kuma ka da a yi abun nan da ake cewa, ‘Sallah ta wuce ta bar wawa da bashi’. Don haka rayuwa sai ka hada da hakuri a kan komi. Ba wanda ba ya kuskure ko matsala ba za ta riske shi ba cikin harkokin rayuwarsa a tsakaninsa da iyalansa, ko makusantansa, ko al’ummar da yake raye a cikinta, ka da don ka rasa wani abu a bikin Sallah ya zama maka damuwa, komi yakan zo ya wuce. Gamuwa da kunci ko wahala ko tsanani da damuwa duk mai yiwuwa ne ga kowa gwargwadon yadda aka kaddara masa, kuma ba wanda zai iya kaucewa abin da aka kaddara masa na sauki ko tsanani a rayuwarsa, don haka a nan mu yi hakuri da duk halin da ake ciki shi ne mafita ga kowa.