Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada bukatar kara azama, a fannin ingiza matakan inganta lafiyar yara, da ci gaban su a dukkanin fannoni, yana mai mika gaisuwar sa ga daukacin yaran kasar Sin, albarkacin ranar yara ta kasa da kasa da ake yin bikin ta duk shekara, a ranar 1 ga watan Yuni.
Xi ya bayyana hakan ne cikin wasikar da ya aike ga cibiyar yara ta kasar Sin a yau Talata, a gabar da cibiyar ke bikin cika shekaru 40 da kafuwa.(Saminu Alhassan)