Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon taya murna ga taron dandalin tattaunawa na Lanting, kan “zamanintarwa irin ta kasar Sin da duniya”, wanda aka shirya a birnin Shanghai.
A cikin sakon na sa, shugaba Xi ya yi nuni da cewa, tabbatar da zamanintarwa, buri ne na al’ummar Sinawa a cikin shekaru dari da suka gabata, kaza lika hakan buri ne na daukacin al’ummomin kasa da kasa, don haka idan ana son cimma wannan buri, ya dace a nemi hanyar da ta dace da hakikanin yanayin da kasa ke ciki.
Hakan ne ma ya sa jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, ta samu hanyar raya kasa da ta dace da yanayin kasar Sin, bayan da ta yi matukar kokari tare da al’ummun kasar ‘yan kabilu daban daban cikin dogon lokaci. Ya ce yanzu haka ana gina kasar Sin mai karfi, tare da farfado da al’ummar Sinawa ta hanyar zamanintarwa irin ta kasar Sin.
Kana kasar Sin tana da burin hada kai da sauran kasashen duniya, tana son samar da sabbin damammaki ga ci gaban duniya, ta yadda za a ingiza gina kyakkyawar makomar bil Adam ta bai daya yadda ya kamata. (Mai fassarawa: Jamila)