• English
  • Business News
Wednesday, August 27, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tsaro Wani Hakki Ne Na Dan Adam

by CMG Hausa
2 years ago
in Daga Birnin Sin
0
Tsaro Wani Hakki Ne Na Dan Adam
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Abokaina barka da karamar Sallah! Na ga wasu hotunan bukukuwan murnar Sallah da wasu abokai suka yi tare da iyalansu, ta shafukan sada zumunta. Na ji dadin yadda suke biki cikin wani yanayi na murna da kwanciyar hankali. Saboda kun san ba a ko ina ake iya yin haka ba.

Yanzu haka a kasar Sudan da ba ta da nisa da kasar Najeriya, ana ci gaba da fama da dauki ba dadi. Kana a Mali da Burkina Faso, su ma sun samu abkuwar hare-hare a kwanakin nan. Ko a wasu yankunan kasar Najeriya ma, hare-haren ’yan fashi da masu neman satar mutane na ci gaba da ci wa jama’a tuwo a kwarya.

  • Xi Jinping Ya Mikawa Dandalin Bayanai Na MDD Karo Na 4 Wasikar Taya Murna

Kowa ya sani, tsaro wani hakki ne na dan Adam, kuma tushen ci gaban al’umma. Saboda idan babu tsaro, ba za a iya rayuwa ba, balle ma a samu ci gaban sauran harkoki.
A wasu wurare, yanayi na tashin hankali ya kori masu neman zuba jari, abin da ya sa ake fuskantar rashin damar raya masana’antu, da karancin guraben aikin yi da za a iya samar wa matasa.

Daga baya, matasan da ba su da aikin yi su kan fara kokarin neman duk wata hanyar samun kudi, har ma wasunsu suka fara karya doka, lamarin da ke kara lalata yanayin tsaron da ake ciki. Ta wannan hanya, wadannan wurare sun tsunduma cikin da’irar faduwa, inda yanayi na yamutsi da talauci ke kara tsananta.

Yayin da a wasu wurare, mabambantan kasashe, da rukunoni ke gwabza fada a tsakaninsu, saboda kowanensu na neman tabbatar da tsaron kai. Sai dai fadan da suke yi ya sa tsaro ya zama wani abu mai nisa, wanda kusan ba za a iya tabawa ba.
Ta la’akari da wannan yanayin da ake ciki ne, ya sa kasar Sin gabatar da shawarar tabbatar da tsaron duniya, a shekara daya da ta gabata.

Labarai Masu Nasaba

Kasar Sin Ta Yi Watsi Da Kiran Shiga Tattaunar Kwance Damarar Nukiliya Tare Da Amurka Da Rasha

Sin Ta Sanar Da Cimma Nasarar Dashen Huhun Alade A Jikin Bil’Adama

Babban makasudin shawarar shi ne, a yi kokarin samar da wani yanayi na tsaro na bai daya. Wato don tabbatar da tsaro a duniyarmu, ana bukatar samun tattaunawa, da hadin gwiwa tsakanin kasashe daban daban.

Dole ne a tabbatar da tsaron kowa, ta yadda tsaron zai iya dorewa. Saboda haka, ya kamata, mabambantan kasashe su kara kokarin musayar ra’ayi da hadin kai, da nacewa ga adalci, da bin ka’idojin kasa da kasa, da neman daidaita rikici kafin ya yi tsamari, ta yadda za a iya tabbatar da tsaron daukacin bil Adama cikin hadin gwiwa.

A nata bangare, kasar Sin ta ba da wannan shawara ta tabbatar da tsaro a duniya, ita ma ta aikata hakan kamar yadda ta fada. Cikin shekarar da ta wuce, mun gane ma idanunmu yadda kasashen Saudiya, da Iran, suka kawo karshen sa-in-sa a tsakaninsu, da farfado da huldar diplomasiyya, bisa sulhun da kasar Sin ta yi, da yadda kasar Sin ta yi kokarin neman sanya kura ta lafa a kasar Ukraine, tare da gabatar da wata muhimmiyar takardar bayani, wadda a cewar Stephane Dujarric, kakakin babban magatakardan MDD, wata muhimmiyar gudunmowa ce ga yunkuruin daidaita rikicin.

Ban da haka kuma, cikin wani dogon lokacin da ya gabata, kasar Sin ta yi kokarin hadin gwiwa da kasashen Afirka, da kasashe masu tasowa na sauran sassan duniya, a bangaren aikin tsaro da ba na gargajiya ba, wanda ya hada da yaki da ta’addanci, da samar da isashen abinci, da aikin jinya, da dai sauransu.

Inda kasar Sin ta tura sojojinta fiye da dubu 50 don halartar aikin wanzar da zaman lafiya da MDD take gudanarwa, da taimakawa kasashen Afirka horar da kwararru masu fasahohin aikin gona, da noman sabbin nau’ikan amfanin gona masu inganci, da samar da alluran rigakafin cutar COVID-19 fiye da biliyan 2.2 ga kasashe da kungiyoyi fiye da 120, da tura dimbin tawagogin likitoci zuwa kasashe daban daban, inda suka samar da hidimar jinya ga mutane kimanin miliyan 290.

Sai dai mun san ba za a iya tabbatar da tsaron duniya ta karfin wata kasa kadai ba. Aikin na bukatar hadin gwiwar kasashe daban daban. A nan, mun gamu da katari, ganin yadda mutanen duniya ke ci gaba da daukaka zaman lafiya da bunkasuwar tattalin arziki, a wannan zamanin da muke ciki.

Yanzu haka, wasu kasashe da kungiyoyi fiye da 80 sun yaba da kasar Sin, da nuna mata goyon baya, kan shawarar da ta gabatar ta tabbatar da tsaro a duniya.

Hakan ya nuna cewa, kasashe daban daban sun fara cimma ra’ayi daya, wato manufar yin babakere a duniya, da ta sa hannu cikin harkokin gida na sauran kasashe, da yin takara cikin wani mummunan yanayi, da ra’ayi na son kai, kawai suna lahanta tsaro na kowa. Yayin da ra’ayin kasar Sin na tabbatar da tsaro na bai daya, ya zama wata manufa ta girmama mutunci na kowace kasa, da hakki na tushe na daidaikun mutane. (Bello Wang)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Tanzaniya Ta Yi Maraba Da Zuwan Tawagogin Yawon Shakatawa Na Sin

Next Post

Sin Ta Kaddamar Da Ranar Samaniya Ta Hanyar Baje Hotunan Duniyar Mars

Related

Kasar Sin Ta Yi Watsi Da Kiran Shiga Tattaunar Kwance Damarar Nukiliya Tare Da Amurka Da Rasha
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Yi Watsi Da Kiran Shiga Tattaunar Kwance Damarar Nukiliya Tare Da Amurka Da Rasha

40 minutes ago
Sin Ta Sanar Da Cimma Nasarar Dashen Huhun Alade A Jikin Bil’Adama
Daga Birnin Sin

Sin Ta Sanar Da Cimma Nasarar Dashen Huhun Alade A Jikin Bil’Adama

53 minutes ago
Shin Mummunan Halin Da Aka Shiga Yayin Yakin Duniya Na II Bai Isa Darasi Ba?
Daga Birnin Sin

Shin Mummunan Halin Da Aka Shiga Yayin Yakin Duniya Na II Bai Isa Darasi Ba?

20 hours ago
Firaministan Kasar Sin Li Qiang Ya Taya Nestor Ntahontuye Murnar Zama Sabon Firaministan Kasar Burundi
Daga Birnin Sin

Firaministan Kasar Sin Li Qiang Ya Taya Nestor Ntahontuye Murnar Zama Sabon Firaministan Kasar Burundi

21 hours ago
Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Gana Da Shugaban Majalisar Dokokin Rasha
Daga Birnin Sin

Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Gana Da Shugaban Majalisar Dokokin Rasha

23 hours ago
Sin Ta Bukaci Japan Ta Waiwayi Tarihin Kutsen Da Ta Yi
Daga Birnin Sin

Sin Ta Bukaci Japan Ta Waiwayi Tarihin Kutsen Da Ta Yi

23 hours ago
Next Post
Sin Ta Kaddamar Da Ranar Samaniya Ta Hanyar Baje Hotunan Duniyar Mars

Sin Ta Kaddamar Da Ranar Samaniya Ta Hanyar Baje Hotunan Duniyar Mars

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Ta Yi Watsi Da Kiran Shiga Tattaunar Kwance Damarar Nukiliya Tare Da Amurka Da Rasha

Kasar Sin Ta Yi Watsi Da Kiran Shiga Tattaunar Kwance Damarar Nukiliya Tare Da Amurka Da Rasha

August 27, 2025
Sin Ta Sanar Da Cimma Nasarar Dashen Huhun Alade A Jikin Bil’Adama

Sin Ta Sanar Da Cimma Nasarar Dashen Huhun Alade A Jikin Bil’Adama

August 27, 2025
Nijeriya Za Ta ÆŠaukaka Da Fasahar Ƙere-Æ™ere Da Tattalin Abinci – Tinubu

Nijeriya Za Ta ÆŠaukaka Da Fasahar Ƙere-Æ™ere Da Tattalin Abinci – Tinubu

August 27, 2025
Sin Da Kasashen Afirka Za Su Rubuta Sabon Babin Hakkin Dan Adam Bisa Ci Gabansu

Sin Da Kasashen Afirka Za Su Rubuta Sabon Babin Hakkin Dan Adam Bisa Ci Gabansu

August 27, 2025
Gwamnatin Imo Ta Amince Da N104,000 A Matsayin Sabon Mafi Ƙarancin Albashin Ma’aikata 

Gwamnatin Imo Ta Amince Da N104,000 A Matsayin Sabon Mafi Ƙarancin Albashin Ma’aikata 

August 27, 2025
Mazauna Kuyello A Jihar Kaduna Na Cikin Zullumin Bayyanar ‘Yan Ta’addar Ansaru

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 8 A Kaduna, Sun Jikkata Wasu

August 27, 2025
An Yi Wa ‘Yar Shekara 18 Fyade Har Lahira A Taraba

‘Yansanda Sun Ceto Mutum 5 Da Aka Sace A Jihar Kebbi

August 27, 2025
Jirgin Ƙasan Abuja-Kaduna Ya Yi Hatsari, Ba A San Halin Da Fasinjoji Ke Ciki Ba

NRC Ta Dakatar Da Sufurin Jirgin Ƙasan Abuja-Kaduna Bayan Hatsarin Da Ya Yi 

August 27, 2025
PDP Na Tattaunawa Da Obi Da Jonathan Kan Yi Mata Takarar Shugaban Ƙasa A 2027 – Moro

PDP Na Tattaunawa Da Obi Da Jonathan Kan Yi Mata Takarar Shugaban Ƙasa A 2027 – Moro

August 27, 2025
Kwalara Ta Kashe Mutum 7 A Zamfara, Sama Da Mutum 200 Sun Kamu Da Cutar

Kwalara Ta Kashe Mutum 7 A Zamfara, Sama Da Mutum 200 Sun Kamu Da Cutar

August 27, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.