A yau Litinin ne shugban kasar Sin Xi Jinping, ya mikawa dandalin bayanai na MDD karo na 4, wasikar taya murnar bude taronsa. A cikin wasikar, Xi Jinping ya nuna cewa, samun bunkasuwa mai dorewa, bukata ce da ya kamata al’ummar Bil Adama ta cimma domin samun wadatarta.
Kaza lika tabbatar da bunkasuwar duniya mai karfi, da kiyaye muhalli yadda ya kamata, muradu ne na daukacin al’ummar duniya baki daya.
Shugaban na Sin ya ce kasarsa na goyan bayan MDD, bisa ajandar samun bunkasuwa mai dorewa ta nan da shekara 2030, da kokarin tabbatar da ita, kuma tana nacewa ga yin kirkire-kirkire, da sulhuntawa, da kiyaye muhalli, da more ra’ayin samun sabbin bunkasuwa, da ma rarraba dabaru, da fasahohin da Sin take da su, na samun bunkasuwa mai dorewa.
Har ila yau, Sin na fatan kara gudanar da hadin kai da kasashe daban-daban, a fannin bayanan duniya, bisa shawarar samun bunkasuwar duniya baki daya, ta yadda za a ingiza ci gaban kasa da kasa.
An bude wannan dandali karo na 4 ne a yau Litinin a birnin Hangzhou na lardin Zhejiang. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp