Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya, ya amince da nadin Zakari Isa Kwami a matsayin mai rikon mukamin Safiyo-Janar da Ibrahim Abubakar Dule a matsayin mai rikon kwarya na babban jami’in kididdiga na Jihar Gombe.Â
Shugaban ma’aikata na jihar, Alhaji Bappayo Yahaya ne ya sanar da amincewar Gwamnan, yana mai bayyana cewa hakan ya biyo bayan ritayar da masu rike da mukaman biyu suka yi ne, kuma ya dace da ikon da aka bai wa gwamna a sashi na 208 karamin sashi (2c) na kundin tsarin mulkin Nijeriya da aka yi wa kwaskwarima.
Ya ce, sabbin nade-naden an yi su ne bisa la’akari da cancanta, aminci da sadaukar da kai da kuma kwarewar da suke da shi a aikin gwamnati, inda ya bukace su da su sanya irin wadannan halaye da kwarewa nasu wajen gudanar da ayyukan su a sabbin mukaman nasu.
Sabon Mukaddashin Safiyo-Janar din Zakari Isa Kwami, ya yi karatun digirin sa a harkar safiyo a Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) Bauchi, kuma ya fara aiki ne a shekarar 2006 a matsayin jami’in filaye kuma ya yi rajista da kungiyar kwararrun safiyo-safiyo ta Nijeriya wato Surveyors’ Council of Nigeria (SURCON) a shekarar 2017. Ya rike mukamai daban-daban har ya kai matsayin babban safiyo na jiha.
A nasa bangaren, mukaddashin babban jami’in kididdigan na jiha, Ibrahim Abubakar Dule, ya yi digirin sa ne a jami’ar Abuja. Ya kuma fara aiki a Jihar Gombe ne a shekarar 2005 a matsayin magatakardan kungiyoyin hadin kai, inda ya yi ta samun karin girma har zuwa matsayin babban magatakardan kungiyoyin hadin kai, daga nan kuma ya koma ofishin kididdiga na Jihar Gombe a matsayin babban jami’in kididdiga.
Dukkanin nade-naden sun fara aiki ne daga ranar 6 ga wannan wata na Afrilun 2023.