Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta yi watsi da bukatar da aka shigar a gabanta ta neman bayar da belin Tukur Mohammed Manu da ake zargi da daukar nauyin ta’addanci.
Alkalin kotun mai shari’a Inyang Ekwo ne ya dauki wannan matakin a zaman kotun aka yi a yau Alhamis, inda ya ce, takardar neman belin Manu babu wasu gamsassun hujjoji a cikinta da za ta sa, kotun ta bayar da belinsa.
- Za A Yi Taron Koli Tsakannin Kasar Sin Da Kasashen Tsakiyar Asiya A Watan Mayu A Xi’an
- Zaben Adamawa: A Hukunta Kwamishinan Zaben Adamawa -Fintiri
Ekwo ya ce, Mamau ya gaza kare kansa, inda ya ce, mai yiwuwa wanda ake tuhumar ya kara aikata wasu laifukan.
Ya ci gaba da cewa, a bisa ka’idar doka idan har wanda ake tukuma ya gaza kare kansa zargin da ake yi masa, zai iya zamo wa gaskiya domin abin da aka gabatar wa kotun ana bukatar karin hujja daga wajen wanda kotun ke tuhuma.
Sai dai, alkalin ya ce wanda kotun ke tuhuma ya yi ikirarin cewa, wajen da hukumar jami’an tsaro ta farin kaya ta jiha ta ajiye shi (SSS), ba zai iya samun kalubalen rashin lafiyar da yake fama da ita ba, inda ya ce, kotun za ta yi duba kan hakan, kafin ta dauki mataki na gaba.
A cewar Ekwo, kotun za ta auna hujjojin don ganin ko wadanda ke tsare da wanda ake tuhumar za su bashi damar zuwa a duba tafiyarsa.
Ya ce, hukumar ta SSS, na da kayan kiwon lafiya da za ta iya duba tafiyar wanda ake tuhumar yadda ya kamata, sai dai, ya bayyana cewa, kotun ba za ta yi jayayya da takarar neman belin zuwa neman lafiyar wanda ake tuhumar ba.
Alkalin ya kara da cewa, idan wadanda ke tsare da wanda ake tuhumar ba su da kayan aikin da za su duba tafiyar wanda ake tuhumar ba, amma za su iya tabbatar da samar masa da asibtin da za a duba tafiyarsa dai-dai da irin ciwon da yake fama da shi, kotun ba za ta iya bayar da belinsa ba.
Ya ci gaba da cewa, a yanzu idan wanda kotun ke tuhuma yaki amincewa da inda wadanda ke ajiya da shi suka samar masa wurin da za a duba tafiyarsa amma asibitin ya kasance matsayin da shi wanda ake tuhumar yake so ba, saboda haka bai da wata hujjar a bayar da belinsa.
Ya ce, wanda ake tuhuma da ke ake tsare da shi a jiha ko a hannun hukumar tsaro kamar mai korafi ko wanda ake tuhuma a hannun DSS, dole ne su fahimci kudin da za a kashe na duba tafiyarsa ya kasance su biya daga aljihun jihar da kuma duba bukatunsa.
Ya ce, hujjar da ke gaban kotun ta nuna cewa, bayan wanda kotun ke tuhumar yaki amincewa da a duba tafiyarsa a asibitin DSS, hukumar ta kai shi kwararren asibitin Arewa da kuma cibiyar kiwon lafiya da ke a Jabi.
Ya ce, a asibitin Arewa an yi masa gwaje-gwajen lafiyarsa yadda ta kamata.
Alkalin ya kara da cewa, DSS ta tabbar da cewa, asibitin ya duba tafiyarsa yadda ta kamata kuma a shirye ta ke, ta biya kudin da aka duba tafiyar Mamu.
Ya ce, DSS ta tabbatar da samar da dama ga Mamu wajen kula da lafiyarsa ta yau da kullum a yayin da yake ci gaba fuskantar shari’a, inda ya ce, bisa wadanan hujojin, maganar bayar da belinsa ba ta taso ba kamar yadda sashen doka na 1 da na 2 na dokar ACJA ta 2015 ta tanada.
Alkalin ya ce saboda haka kotun ta yi watsi da takardar bukatar bayar da belin nasa.
Gwamnatin tarayya ce ta gurfanar da Mamu a ranar 21 ga watan Maris kan tuhuma 10 ciki har da ta daukar nauyin ta’addanci da sauransu.