Yayin da yake yin karin haske ko bayani kan yadda ake samun karuwar kansar makogwaro a yammacin Turai Likitan tiyata Dr Hisham Mehanna ya bayyana cewa jima’in da wasu ke yi wa mata ta baki wato yadda suke amfani da harshe suna sawa cikin farjin mace, na da ban mamaki da daure kai, domin kuwa hadarin hakan ya fi na cututtukan da ake dauka ta shan Taba da Giya.
A wata mukalar da ya rubuta, Dr Mehanna ya ce Kansar Oropharyngeal (tana kasancewa tsakanin wasu kofofi biyu da makogwaro) yanzu ta zama wani al’amari da za a iya cewa tamkar gidan kowa akwai fiye da kansar mahaifa a kasarAmurka da hadaddiyar Daular Larabawa.
Kamar yadda ya ce, dalilin da yasa ake kamuwa da kansar shi ne wata kwayar cuta ta Dan’adam mai suna papillomabirus (HPB), ana daukar ta ce ta hanyar jima’in da ake yi da baki, inda hakan ke matukatr illa ga galibin wadanda suke aikata wannan dabi’a.
“Nazarin da aka yi ya nuna irin nau’in jima’i da baki ya fi faruwa ne a wasu kasashe”.
“Wani abu daban shi ne yawancin wadanda suka kamu da cutar HPB suna iya rabuwa da ita gaba daya, sai dai kuma wasu sun kasa gane hanyar da za su rabu da cutar watakila hakan ta kasance ne saboda irin tsarin kwayoyin halittarsu. Irin wadancan maras lafiyar da ke fama da kwayar cutar tana iya sake ci gaba da maimaita kanta a cikin kwayoyin halittarsu, da a sanadiyar haka tana iya sa kwayoyin halitta na wanda ya kamu da cutar ta rikide ta zama cutar daji ko kansa.
“Wadanda suka yi jima’i ta baki kamar sau shida ko fiye da haka a rayuwarsu suna da yiwuwar kamuwa da kwayar cutar da kashi takwas da digo biyar 8.5 fiye da wadanda ba su taba kwatantawa ba.”
Sai dai kuma ya ce, akwai shaida da ba ta kai tsaye ba da ta nuna allurar kwayar cutar ta HPB tana taimakawa wajen hana kamuwa da ita.