- Burina Na Ga Kumurci Na Yi Shirin Fim Da Shi
- Abin Da Ya Fi Ba Ni Dariya A Shirin Dadin Kowa
Shafin Rumbun Nishadi ya zakulo muku daya daga cikin fitattun Jaruman fina-finan Hausa da ke taka rawa a yanzu, Jarumar da ke haskawa a cikin shiri me dogon zango na Arewa24 na ‘Dadin Kowa’. Jaruma SADIYA MUSA wadda aka fi sani da AZUMIN MALAM NATA’ALA ta bayyana wa masu karatu, irin matsalolin da suke fuskanta tare da bayyana babban burin da ya dade yana addabarta cikin zuciya, wanda kuma take sa ran cimma sa nan ba da jimawa ba. Jarumar ta yi kira ga masu yunkurin shiga cikin masana’antar Kannywood, har ma da wadanda ke cikin dan samun ci gabansu cikin masana’antar, har ma da wasu batutuwan da suka shafi sana’arta ta fim. Ga dai tattaunawarta da wakiliyarmu RABI’AT SIDI BALA kamar haka:
Da farko masu karatu za su so su ji cikakken sunanki tare da dan takaitaccen tarihinki…
Ni sunana Sadiya Musa amma an fi sanina da Azumin Malam Na Ta’ala. Ni ‘Yar asalin Jihar Kano ce a karamar hukumar Tarauni, ina zaune a unguwar Daurawa. Nayi Firamare a Daurawa Firamare, Nayi Sakandare a ‘Gezawa Gobt Girls Teacher’s College’. Nayi aure amman ban samu haihuwa ba, wannan shi ne takaitaccen tarihina.
Me ya ja hankalinki har kika tsunduma harkar fim?
To wallahi ni dai kawai sha’awa ce, dan ina da sha’awar harkar tun ina karama.
Za ki kamar shekara nawa da fara fim?
To a takaice zan yi kamar shekara shida 6.
Ya gwagwarmayar shiga masana’antar ta kasance?
To ni dai da sauki ba kamar yadda wasu suka gamu da abu daban-daban ba, dan daga kungiya na fara.
Idan na fahimce ki a kungiyanyance kika fara gabatar da shirye-shirye daga bisani kika tsunduma cikin masana’antar ko ya abin ya ke?
Eh! na fara da kungiyar ‘Nurul Zaman Dramatic Forum’, daga nan na tafi kungiyar T.C.P dake Tarauni sai na tafi kamfanin ‘Mai Gizo Film Production’ daga nan kuma sai na tafi ARTB, na fara ‘Program’ din ‘Ciki Da Gaskiya’ da Zaman Duniya da sauransu.
Lokacin da za ki fara fim din, ko akwai wani kalubale da kika fuskanta wajen iyaye?
Eh! to ni da girmana na fara ban samu matsala ba, dan tun ina makaranta ina ‘Hausa Club’.
Me ya fara baki tsoro game da fim kafin ki fara?
Abin da ya fara ba ni tsoro shi ne ‘Camera’.
Kina nufin yadda za ki tsaya kina magana ana dauka kenan shi ya fi razanaki, ko ya kike nufi?
Eh! kuwa kamar kin sani.
Bayan wasannin kungiya da kika yi, da wanne fim kika fara a cikin masana’antar Kannywood?
Juyin sarauta na Hajiya Balaraba Ramad Mohd.
Wacce rawa kika taka cikin shirin, kuma ya karbuwar shirin ya kasance ga masu kallo?
Ya karbu sosai, a Uwar Soro na fito, wanda da dama mutane da haka suke kira na, ya samu Award wajan sau 5.
Daga lokacin da kika fara kawo yanzu kin yi fina-finai sun kai kamar guda nawa?
Wallahi banace ba, dan suna da yawa, yanzu dai muna kam wani mai suna Lulu da Andalu na T.Y Shaba.
Ya akai kika tsinci kanki a cikin shirin Dadin Kowa?
Sai na ce rabo ne kawai, wadda take yin Azumi ita ta daina saboda matsala da ta samu to sai aka kira ni in gwada, ina gwadawa aka ce yayi ta hannun Dart Turufa
Ya kika ji a lokacin da kike kokarin gwadawa?
Lokacin ban ji tsoro ba da na fara, lokacin ba tsoro.
Wanne waje ne ya fi ba ki wahala a cikin shirin Dadin Kowa, kuma wanne waje ne ya fi saka ki dariya a cikin shirin, haka kuma wanne waje ne kike jin ranki na baci idan kin tuna duk a cikin shirin?
Kawai inda yake ban dariya shi ne inda malan yake nuna bambanci.
Kina jin shirin kamar gaske ne, ko kuwa wani abu ne daban wanda ya ke saki dariya idan yana nuna bambancin?
Wallahi in ina yi bana daukar sa wasa da gaske nake dauka.
Kafin ki fara fim ko akwai Jarumi ko Jarumar da take birge ki wadda har kike jin dama ki zama kamar ita ko kamar shi?
Ina son Kumurci gaskiya.
Wanne irin aktin ne nasa yake birge ki a lokacin?
Ni tuntuni kawai komai ya yi birge ni yake.
Idan aka ce a gaba daya fina-finan da kika fito wanne ne bakandamiyarki wanda kika fi so, wanne za ki dauka?
Sai dai biyu, ‘Juyin Sarauta’ da ‘Dadin Kowa’, sabida da su na yi suna.
Ko akwai wani kalubale da kika taba fuskanta game da fim?
A’A! Sai dai ba ka rabo da mutane marasa fahimta, wasu su zage ka wasu su yabe ka, amman masoyan sun fi yawa.
Toh! Ya batun nasarori fa?
Kai! Alhamdulillah an samu nasarori sosai sai dai godiya.
Gari nawa ko kasa nawa kika taba zuwa sanadiyyar fim?
Gari bakwai 7, irinsu; Lagos, Niger, Ghana, Port Harcourt, Cameroon.
Ya kika dauki fim a wajenki?
Na dauki fim sana’a.
Bayan fim kina wata sana’ar ne?
Eh! ina sai da kayayyaki kamar; Zannuwa da Turare da dai sauransu.
Wanne abu ne ya taba faruwa da ke na farin ciki ko akasin haka wanda ba za ki taba iya mantawa da shi a rayuwa ba?
To gaskiya na farin ciki ne ya faru da ni, saboda abin farin ciki ne ka ga mutum mai mulki ko mai arziki ya rika rawar jiki idan ya gan ka saboda kauna, sannan duk inda ka je kana da alfarma ta sanadin fim, to wannan abin yana sani farin ciki sosai.
Kamar wanne irin rawa kika fi yawan takawa, kuma wanne irin rawa ne bakya son taka shi sai dan ya zama ke din ce za ki taka?
Gaskiya na fi san ‘acting’ din masifa saboda shi na saba, wanda ba na so a sani a Bora wadda miji ba ya so. Gaskiya kamar da gaske nake ji, saboda ki zama Bora ba dadi ko a wasa ne.
Da wanne jarumi ko jaruma kika fi son a hada ki fim tare?
Duk da wanda aka hada ni ina iya yi ban da zabi, Na gaya miki Jarumina Kumurci ne ban taba aiki da shi ba.
Kun taba haduwa bayan da kika shiga cikin masana’antar?
A’a! lokacin da yake fim ba na yi, lokacin da na fara kuma ya dan daina, amman yanzu zai san ni za mu hadu mu gaisa nan ba da dadewa ba.
Ya alakarki take da sauran abokan aikinki, da kuma sauran kawayenki da kuka taso tare tun na kuruciya?
Alakarmu da su me kyau ce gaba daya.
Me za ki ce da masu kallo musamman masu yi muku kallon kun ki yin aure, ko kun ki zama gidan mazajenku?
To sai mu ce musu su yi hakuri komai na Allah yana da iyaka, su dai su rika yi mana fatan alkairi dukkanmu daya ne mu da su.
Ya kike da sauran al’umma, musammn irin wadanda idan kika fito daga gida za su rinka tare ki, ko su rinka kallonki, ko makamancin hakan, shin kikan fuskanci wani kalubale daga gare su ko kuwa kalau kike fita?
Eh! gaskiya muna haduwa da masoya kala-kala wani lokacin ma idan sun yi min yawa na kan zura da gudu, dan wallahi idan na je kasuwa kamar nayi kuka saboda jama’a, wataran inda na je haka nake dawowa ban sai komai ba, Masoya suna da dadi suna da wuyar sha’ani sai dai hakuri.
Za ki ga wasu na saka Nikab in za su fita sabida kauce wa hakan, shin ke ma kikan yi hakan ko kuwa?
Cab! ko kin sa idan daya ta gane ki shikenan, ina sawa, dan wasu muryar ki kawai za su ji su gane ki.
Ya batun Soyayya, ko akwai wanda ya taba cewa yana sonki cikin masana’antar?
A’A! soyayya ai sai yara Tsofai-tsafai da ni, bana yi, bar mu a haka dai.
Idan wani ya ce yana sonki zai aure ki cikin masana’antar shin za ki yarda ki amince, ko kuwa ba ki da ra’ayin hakan?
Hhhhhh… Aure Ai yin Allah ne idan Allah yayi sai a yi.
Toh! Ya batun aure, yaushe kike sa ran kara yi?
In Allah ya kawo shi sai a yi.
Misali yadda kike tsaka da yin shirin Dadin kowa, wani ya fito zai aure ki, za ki katse shirin, ko kuwa za ki ci gaba?
Ah! Da gudu ma ai Aure ya fi karfin wasa.
Yanzu misali a ce kin yi aure kin haifi ‘ya ta girma, sai ta ce tana sha’awar shiga harkar fim, shin za ki barta tayi ko kuwa ba ki da ra’ayin hakan?
Toh! ai fim sana’a ce.
Mene ne burinki na gaba game da fim?
Burina na ga Kumurci na yi fim da shi tun da lokacin da na san shi shi bai san ni ba.
Me za ki ce da masu kokarin shiga cikin masana’antar har ma da sauran wadanda suke ciki?
Kamun kai, ladabi, kasan girman mutum ko ya yake, ko da ba shi da komai, dan dare daya Allah kan yi bature. Kiyaye mutuncin ko a ina kike, Allah yana kallonki ko da ba kya ganinshi.
Ko kina da wani kira da za ki yi ga gwamnati game da ci gaban masana’antar?
Eh! fata na gwannati ta shigo cikin harkar, ta kara ingantata, ta tallafe ta, wataran za ta yi Alfahari da ita.
Me za ki ce da masoyanki?
Ina godiya da kaunar da kuke min, Allah ya saka da alkairi na gode.
Me za ki ce ga makaranta wannan shafi na Rumbun Nishadi?
Masoya masu tarin yawa sannunku da kokari da kulawa, sannuku da karatu, na san kauna ce ta sa haka, Allah ya kara kauna da soyayya, mun gode Allah ya biya mana duk bukatunmu na alkhairi baki daya.
Me za ki ce da ita kanta Jaridar Leadership Hausa?
Gaskiya LEADERSHIP Hausa na gode Allah ya sa ta fi haka, Allah ya kara daukaka, sharrin mutum, hassada, makirci, Allah ya kare ku, gaba dai-gaba dai ina yi mata fatan nasara ko ina ta shiga.
Ko kina da wadanda za ki gaisar?
Da farko Mamana, kawayena da aminiyata Saratu da Ahmad.