- Kwankwaso Ya Kyale Abba Ya Yi Mulki Ba Jingina Tsohon Mulkinsa Da Wannan Ba – Aruwa
- A Yi La’akari Da Alfanu Ko Akasinsa Wajen Rushe Abun Da Gwamnati Ta Aiwatar – Kwamared Ishak
Batun ce-ce-ku-cen da ake ta yamadidinsa a Jihar Kano yanzu bai wuce wasu kalamai da tsohon gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Muasa Kwankwaso na nuna yiwuwar rushe wasu wuraren da gwamnatin mai barin gado ta bayar aka gina ko ta gina da kanta, sannan kuma ana hangen yiwuwar kila a dawo da bara bana ta hanyar kokarin da wasu ke yi na ganin an dawo da tsohon sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, wanda Gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta sallama bayan samun takun saka a tsakaninsu.
A kan haka yanzu Kanawa kowa ya zuba na mujiya domin ganin yadda za ta kaya tsakanin gwamnatin mai jiran gado da mai barin gado, musamman jin yadda jagoran darikar Kwankwasiyya ke furta wasu kalamai a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai.
An dai ji Kwankwaso yana karin haske da aka tambayeshi shin mene gaskiyar lamarin da ake jita-jita cewa Gwamnatin NNPP za ta rushe masarautu hudun da Ganduje ya kirkira tare da maido da tsohon sarki, Muhammadu Sanusi kan karagar mulki Kano.
A nan ne aka ji Kwankwaso na cewa batun masarautu ko cire tsohon sarki abu ne da suke kyautata wa sabon gwamna zaton zai yi nazari tare da duba yadda al’amarin ke gudana, domin samo ingantcciyar hanyar wawaware wannan matsala.
Haka kuma kan batun rushe-rushen wuraren da gwamnati mai barin gado ta bayar aka gina, a nan ma an ji Kwankwason tun kafin cin zaben jam’iyyar tasa yana ikirarin cewa duk wanda aka bashin fili ya gina a wuraren da ba su dace ba, ko hawa 100 ya gina sunan sa rusasshe, har ake misali da filin idi, Ganuwar Kano, kasuwanni, masallatai da makarantu, wanda a ganinsu watandar su aka yi ga masu uwa a gindin murhu.
Ko a lokacin ziyarar ta’aziyyar da Kwankwaso ya je wa attaijrin nan, Alhaji Aminu Alhassan Dantata a gidansa da ke Unguwar Koki a kan hanyarsa ta isa gidan zababben wakilin karamar hukumar Birni da kewaye, an ji Kwankwaso na tsine wa wani wanda ya ce ya yi gini a kan hanya.
Ya ce shi ne maibai wa gwamna shawara, saboda haka zai bai wa zababben gwamna shawarar lallai a rushe ginin da wannan mutum ya yi domin fitar da hanya dodar.
Wadannan dama sauran kalaman jagoran Kwankwasiyyar ya sa yanzu siyasar Kano ke kara dumama. Duk wanda ya san Kwankwaso ya san shi da kafiya kan abin da ya kudurta a zuciyarsa.
Misali kan batun rushe-rushe, lokacin da ya samu nasarar dawowa a matsayin gwamnan Kano zango na biyu, bayan rantsar da shi da aka yi, kungiyar ‘yan kasuwar Jihar Kano sun kai masa ziyarar taya murna, inda aka gudanar da taron a wani fili da ke cikin fadar gwamnatin Kano. Fitowarsa ke da wuya wurin tarbar wadannan ‘yan kasuwa, sai wuri ya rude da kururuwa ana ta fadin “Filin Kofar Na’isa, Filin Kofar Na’isa, a nan Kwankwaso ya yi shiru har sai da aka dan lafa, sannan ya ce “Baku san Rabi’u Musa Kwankwaso ba, ai wannan fili so muke sai gini yakai tsawon linta kawai sai mu rushe.”
A daren wannan rana da misalin karfe 1:00 na dare ya dira a wannan fili kuma ya rusheshi baki daya.
Wannan tasa Kanawa ke ta ce-ce –ku-cen kan irin wadannan kalamai na Kwankwaso wanda a baya haka ya dinga fada kuma yana samun dama sai ya aiwatar da manufarsa.
Wani mai fashin baki kan harkokin siyasar Jihar Kano, Kwamared Ishak Ganduj Albasa ya bayyana cewa lamarin irin wannan dole sai an dubi alfanun abin da ake cewa za a rushe, domin idan wuraren da ake cewa Kwankwaso zai rushe su, sai a duba mene alfanunsu ga jama’a da kuma tattalin arzikin Jihar ta Kano.
A cewarsa, taba wasu wuraren tamkar yunkurin kassara tattalin arzikin al’ummar Jihar Kano ne, musamman idan aka dubi yawan mutanen da ke cin abinci a ire-iren wadannan wurare.
Ya ce kuma idan wuraren da aka gina an ginasu a wuraren amfanin al’umma ne kamar makabartu, asibitoci da makarantu, babu shakka a hangesa ba wata gwamnati da za ta bari a yi watandar wuraren bizne mutane, ko wuraren ibadu da makarantun al’umma.
Da yake tsokaci kan bautun ce-ce-ku-cen da ake cewar wai za a rushe masarautu, a nan ma ya kada baki ya ce dole sai an kalli irin amfanin da wadannan masarautu suka samar a yankunan da aka yi su, kawai ba za a yi amfani da siyasa wajen aiwatar da abubuwan da suke amfanar da al’umma ba.
Hakazalika ya ce suma bangaren masarautun dole su yi kokarin tsayawa a bangaren sha’anin sarautunsu, kar su shiga siyasa, domin shigarsu siyasa ke sawa ‘yan siyasa ke kallon gudunmawar da suka ba su wajen neman hanyar saka masu, to dole sai an yi karatun ta nutsu wajen daukar kowane irin mataki kan wadannan masarautu.
Shi kuwa kakakin jam’iyyar APC na Jihar Kano, Honarabul Ahmed Aruwa ya bayyana cewa kalaman Kwankwaso tsohon ya yi ne, ya kyale Abba a ga nasa tunanin ba ya jingina tsohon mulkinsa da wannan ba.
Honarabul Aruwa ya ce matsayarsa kan kalaman da jagoran Kwankwasiyya ke yi da cewa tsohon ya yi ne, domin duniya tuni ta ci gaba an daina irin wadannan kalaman, musamman ikirarin da yake kan masarautu, domin kamata ya tuna gwamnati gaskiya ce, shi ma ya yi irin tasa gwamnatin.
A cewarsa, idan Kwankwaso ya tuna batun tsohon sarki da yake yi, ai lamari ne da ya shafi karya wasu ka’idoji, kuma aka gudanar da bincike aka samu tsohon sarkin da laifi.
Ya ce a ganinsa bai kamata Kwankwaso ya dinga siyasantar da harkar masarautun Kano ba, domin idan yana ganin yanzu wata dama ce ya samu zai rushe wadancan masarautu, shi kenan su tabbata za su yi?. Kenan da zarar nasu lokacin ta kare idan wani ya zo shi ma sai rushe wanda suka kawo ya dawo da nasa.
Ya kara da cewa kenan nan gaba suma masarautun sai sun din ga buga fastar neman duk wanda ke son mulkin Kano sai ya zabi sarkin da ke kan karagar mulkin Kano.
Ya ce wannan ba wani abu bane illa kokarin mayar da hannun agogo baya, sannan kuma kokarin ne na kassara tattalin arzikin Kano, idan Kwankwaso zai tuna abin da Bola Ahmad Tinubu ya yi wa Jihar Legas yake tunkaho da shi kuma aka gani har aka zabe shi a matsayin shugaban kasa, mai zai hana shi ma Kwankwaso ya dinga tunkaho da wani abu da ya yi wa Jihar Kano domin yin alfahari da shi, kawai sai ya buge da jingina tsohuwar gwamnatinsa da wannan, kamata ya yi yabar wanda ake ikirarin an zabe shi ya fito da nasa manufofin.
Abin da ake jira shi ne, yanzu ba a san maci tuwo sai miya ta kare, lokaci ne kawai kila zai warware wannan ce-ce-ku-ce. A halin yanzu makonni kalilan suka rage a rantsar da sabuwar gwamnati, sannan kuma ita ma jam’iyyar APC mai barin gado a Jihar Kano tuni ta garzaya kotu domin kalubalantar nasarar NNPP a gwamnan Jihar Kano, bisa wasu kurakurai da suke ganin an tabka a lokacin zaben.