Sakatare-janar na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, wanda kuma shi ne shugaban kasar, kana shugaban kwamitin sojan kasar, kuma shugaban kwamitin koli kan harkokin kudi da tattalin arziki, Xi Jinping, ya jagoranci zama na farko na kwamitin koli kan harkokin kudi da tattalin arziki karo na 20 da yammacin yau Jumma’a 5 ga wata.
Shugaba Xi ya gabatar da muhimmin jawabi a wajen zaman, inda ya jaddada cewa, tsarin gudanar da sana’o’i irin na zamani, babban tushe ne a fannin fasaha ga wata kasa ta zamani, kuma ya zama dole a maida hankali wajen raya sassan tattalin arziki dake shafar kayayyaki na zahiri, a yayin da ake bunkasa tattalin arziki, a wani kokari na aza tubali mai inganci ga cimma burin gina kakkarfar kasar Sin, dake bin tsarin gurguzu mai wadata, da bin tsarin demokuradiyya da wayewar kai irin ta zamani zuwa shekara ta 2049.
Kana, shugaban ya ce samar da ci gaba ga al’umma, shi ne babban al’amari dake shafar farfado da babbar al’ummar kasar ta Sin.
Don haka, ya dace a maida hankali wajen kyautata ingancin al’ummar kasar, domin taimakawa ayyukan zamanantar da kasar. (Murtala Zhang)