Babban sakataren kwamitin kolin JKS kuma shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da wakilan babban taron sada zumunta tsakanin tawagogin Sinawa mazauna kasashen ketare na kasa da kasa karo na 10 a babban dakin taron jama’a dake birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin yau Litinin da safe, inda ya isar da fatan alheri ga Sinawa mazauna ketare dake fadin duniya.
Babban taron sada zumunta tsakanin tawagogin Sinawa mazauna kasashen ketare na kasa da kasa, muhimmin dandali ne na cudanyar dake tsakanin Sinawa mazauna ketare. Babban taken wannan babban taro shi ne “Sada zumunta tsakanin kasar Sin da sauran kasashen duniya domin ingiza ginawar kyakkyawar makomar bil Adama ta bai daya”, wanda ya samu halartar jagororin tawagogin Sinawa mazauna ketare da yawansu ya kai 500. (Mai fassarawa: Jamila)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp