Zababben Sanatan daga Kano ta Kudu a jam’iyyar NNPP, Abdurahman Kawu Sumaila, ya gargadi zababben shugaban kasa, Bola Tinubu ya gujewa munafukan da za su yaudare shi wajen daukar matakan ba ba su dace ba kan gudanar da shugabancin majalisar.
Ya bayyana hakan ne ga manema labarai a ranar Talata a Abuja, inda ya yi nuni da cewa, hanya daya da ‘yan majalisar ta 10 za su iya magance kalubalen da kasar nan ke fuskanta shi ne, yin amfani da kundin tsarin mulkin kasar nan.
- ‘Yansanda Sun Hallaka ‘Yan Bindiga 3, Sun Kwato Bindigogi A Zamfara
- Mutum 15 Sun Mutu A Hatsarin Jirgin Ruwa A Sakkwato
A cewarsa, akasarin ‘yan majalisar na nuna ki ga yin shugabanci na shiyya da APC ke son yi, inda ya kara da cewa, “muna ci gaba da tattaunawa da Sanatoci 109 ina kuma mai ba ku tabbacin cewa, muna da yawan adadin ‘yan majalisar da ba za su aminta a dora mana shugaban da ba ma so a majalisar wakilai ko majalisar dattawa ba.
Ya kara da cewa, “muna son ci gaba da tuntuba, domin abin da muke cewa shi ne Nijeriya na fuskantar kalubale da dama kuma muna da kundin tsarin mulkin da za mu iya yin amfani da shi don lalubo mafita kan kalubalen.
Ya sanar da cewa, “Tinubu ya bar mu zauna mu yi abin da ya dace, musamman abubuwan da za su hada kan kasa, farin ciki da kuma ci gaban kasar nan.”
Kawu ya bayyana cewa, “muna tare da shi a lokacin da taka wa Jonathan birki kan dora shugabanci a majalisar wakilai, saboda haka kar ka bari munafukan ‘yan siyasa su yi maka katsa-landan domin ba za mu bari hakan ya faru a majalisa ta 10 ba.”