• Leadership Hausa
Sunday, December 3, 2023
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

‘Yansanda Sun Hallaka ‘Yan Bindiga 3, Sun Kwato Bindigogi A Zamfara

by Hussein Yero
7 months ago
in Labarai
0
‘Yansanda Sun Hallaka ‘Yan Bindiga 3, Sun Kwato Bindigogi A Zamfara
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Rundunar ‘yansandan Jihar Zamfara ta kashe ‘yan bindiga uku tare da kwato bindiga kirar AK-49 da kuma bindigar famfo a wani samame da ta kai wa ‘yan bindigar a cikin kananan hukumomi Tsafe da Bakura.

Sabon kwamishinan ‘yansandan Jihar, Muhammed Bunu ne, ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a hedikwatar rundunar da ke Gusau, babban birnin jihar a ranar Laraba.

  • ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 3 A Benuwe
  • Mutum 15 Sun Mutu A Hatsarin Jirgin Ruwa A Sakkwato

Kwamishinan ya dauki alkawarin yakar masu aikata miyagun laifuka, “Kuma wannan shi ne kudirin babban Sufeto-Janar na ‘yansandan Nijeriya, Usman Alkali Baba na ganin an kare rayukan al’umma a fadin kasar nan baki daya.”

Bunu ya kuma yaba wa ‘yan jarida bisa hadin kai da goyon bayan da suke bayar wa wajen ganin an kawo karshen masu aikata laifuka da suka addabi Jihar Zamfara.

Kwamishinan ya bayyana cewa, ‘yan fashi da makami, hare-haren ramuwar gayya, sace-sace da garkuwa da mutane don neman kudin fansa, da kuma bangar siyasa a matsayin kalubalen tsaro da ke addabar jihar ta Zamfara, kuma sai yi kokarin kawo karshensu.

Labarai Masu Nasaba

Gwamnatin Tarayya Ta Nemi Kamfanin Nokia Ya Zuba Jari Wajen Karfafa Kimiyyar Sadarwa A Nijeriya

Shirin Rage Tsadar Rayuwa: Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Biyan Sabon Tsarin Albashi Daga Afrilun 2024 – Minista

Rundudar ‘yansandan da ke karkashin sa za su sauke nauyin da ya rataya a wuyansu kamar yadda ya dace da da’a, “Ba za mu amince da cin zarafin dan adam, cin hanci da rashawa da sauran ayyukan da suka saba wa doka ba.”

Kwamishinan ya yi kira da a ci gaba da ba da goyon baya, hadin kai, da hadin gwiwa daga kowa da kowa ta hanyar ba da bayanai masu amfani a kowane lokaci ga ‘yan sanda ga masu aikata laifuka domin daukar matakin gaggawa.

Tags: 'YansandaBindigogiMakamaiYan bindigaZamfara
ShareTweetSendShare
Previous Post

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 3 A Benuwe

Next Post

Zababbun Sanatocin APC Na Arewa Ta Tsakiya Sun Ki Amincewa Da Mukaman Shiyya

Related

Gwamnatin Tarayya Ta Nemi Kamfanin Nokia Ya Zuba Jari Wajen Karfafa Kimiyyar Sadarwa A Nijeriya
Labarai

Gwamnatin Tarayya Ta Nemi Kamfanin Nokia Ya Zuba Jari Wajen Karfafa Kimiyyar Sadarwa A Nijeriya

3 hours ago
Tinubu
Labarai

Shirin Rage Tsadar Rayuwa: Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Biyan Sabon Tsarin Albashi Daga Afrilun 2024 – Minista

5 hours ago
An Kori Jaruma Daga Fim Saboda Wallafa Sakon Goyon Bayan Falasdinawa
Labarai

An Kori Jaruma Daga Fim Saboda Wallafa Sakon Goyon Bayan Falasdinawa

9 hours ago
Bayan Sace Fiye Da Mutum 100 A Zamfara: Kauyukan Da ‘Yan Bindiga Suka Sanya Wa Haraji Na Fuskantar Barazana
Kotu Da Ɗansanda

Bayan Sace Fiye Da Mutum 100 A Zamfara: Kauyukan Da ‘Yan Bindiga Suka Sanya Wa Haraji Na Fuskantar Barazana

13 hours ago
Duk Likitan Mata Na Kula Da Mara Lafiya 6,000 Maimakon 400 A Nijeriya -SOGON
Labarai

Duk Likitan Mata Na Kula Da Mara Lafiya 6,000 Maimakon 400 A Nijeriya -SOGON

18 hours ago
Yadda Majalisar Dinkin Duniya Ta Kammala Shirin Yaki Da Cin Zarafin Mata A Nijeriya
Labarai

Yadda Majalisar Dinkin Duniya Ta Kammala Shirin Yaki Da Cin Zarafin Mata A Nijeriya

19 hours ago
Next Post
Shirin APC Na Zabar Sabon Kakakin Majalisar Wakilai Ya Tada Kura

Zababbun Sanatocin APC Na Arewa Ta Tsakiya Sun Ki Amincewa Da Mukaman Shiyya

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Tarayya Ta Nemi Kamfanin Nokia Ya Zuba Jari Wajen Karfafa Kimiyyar Sadarwa A Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Nemi Kamfanin Nokia Ya Zuba Jari Wajen Karfafa Kimiyyar Sadarwa A Nijeriya

December 2, 2023
Hizba Ta Gana Da Kungiyar Masu Bege, Ta Bukaci Su Tsabtace Harshe

Hizba Ta Gana Da Kungiyar Masu Bege, Ta Bukaci Su Tsabtace Harshe

December 2, 2023
Kasar Argentina Ta Ba Shugaban CMG Lambar Yabo

Kasar Argentina Ta Ba Shugaban CMG Lambar Yabo

December 2, 2023
Tinubu

Shirin Rage Tsadar Rayuwa: Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Biyan Sabon Tsarin Albashi Daga Afrilun 2024 – Minista

December 2, 2023
Furodusoshin Kannywood Sun Yi Taron Kawo Gyara A Masana’antar

Furodusoshin Kannywood Sun Yi Taron Kawo Gyara A Masana’antar

December 2, 2023
Masani: Zamanantarwa Irin Ta Sinawa Wani Sabon Salo Ne Na Wayewa

Masani: Zamanantarwa Irin Ta Sinawa Wani Sabon Salo Ne Na Wayewa

December 2, 2023
Firaministan Cuba: Shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya Za Ta Amfanawa Duk Duniya

Firaministan Cuba: Shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya Za Ta Amfanawa Duk Duniya

December 2, 2023
Dambarwar Zabe: Laifin Wane Ne, Jam’iyyu, Lauyoyi Ko Alkalai?

Dambarwar Zabe: Laifin Wane Ne, Jam’iyyu, Lauyoyi Ko Alkalai?

December 2, 2023
CGTN: Kashi 90 Na Masu Kada Kuri’ar Jin Ra’ayi Sun Bukaci Burtaniya Da Ta Maido Da Kayayyakin Tarihi

CGTN: Kashi 90 Na Masu Kada Kuri’ar Jin Ra’ayi Sun Bukaci Burtaniya Da Ta Maido Da Kayayyakin Tarihi

December 2, 2023
An Bayyana Jigo Da Tambari Na Shirin Telabijin Na Musamman Na Murnar Bikin Bazara Na 2024 Na Kasar Sin

An Bayyana Jigo Da Tambari Na Shirin Telabijin Na Musamman Na Murnar Bikin Bazara Na 2024 Na Kasar Sin

December 2, 2023
Advertise with us

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.