Yayin taron manema labarai na yau Litinin da kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Wang Wenbin ya jagoranta, an nemi jin ra’ayin kasar game da yiyuwar taron kungiyar G7 na Hiroshima, ya fitar da wata sanarwa dangane da tsaron tattalin arziki, dake jaddada bukatar kauracewa dogaro da Sin a fannoni kamar na kananan na’urorin laturoni na Semiconductor da ma muhimman ma’adinai.
A martaninsa, Wang Wenbin ya ce idan har da gaske kungiyar G7 ta damu da batun tsaron tattalin arziki, to kamata ya yi kasashen kungiyar su bukaci Amurka ta daina fakewa da batun tsaron kasa tana danne ci gaban sauran kasashe, da daina yin gaban kanta wajen kakaba takunkumai da tilastawa kawayenta shiga wani rukunin taron dangi da kuma daina yunkurin raba duniya gida biyu, mai tsare-tsare biyu.
Har ila yau, da yake tsokaci game da batun da ya shafi sauraron ra’ayin jama’a kan yankin HK da rahoton kwamitin kula da harkokin Sin na majalisar wakilan Amurka, Wang Wenbin ya ce dama sun dade suna tsokaci kan harkokin cikin gidan kasar Sin, da jirkita gaskiya da gangan da kai wa Sin hari da bata mata suna, lamarin da ba shi da kima a siyasance ko kadan. (Mai fassarawa: Mustapha Fa’iza)