Gwamnatin tarayya ta amince da bayar da lasisin ga sabbin jami’o’i 37 a Nijeriya.
Jami’o’in sun samu sahalewar ne yayin wani zama na musamman da Majalisar Zartarwar Nijeriya ta yi a ranar Litinin.
- Ma’aikatar Hukumar Shige Da Fice Ta Nijeriya Na Gayyatar Jarabawar Daukar Aiki
- Sudan: Jami’o’in Nijeriya Sun Sha Alwashin Bai Wa Daliban Da Aka Kwaso Guraben Karatu
Ministan Ilimi, Adamu Adamu, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a fadar gwamnatin bayan wani taron gaggawa da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, ya jagoranta a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Ya kara da cewa sabbin Jami’o’in kawo yanzu sun kai adadin 72 da gwamnatin Buhari ta bayar da lasisin su tun daga shekarar 2015.
Sai dai Ministan bai bayyana sunayen jami’o’in ba, inda ya bayyana cewa daya daga cikinsu jami’a ce ta yanar gizo, wacce ita ce irinta ta farko mai zaman kanta a Nijeriya mallakin wata mata daga jihar Bauchi.
A cewarsa, ana sa ran Jami’ar za ta dauki nauyin mata Musulmi ‘yan Arewa da ba sa so ko kuma aka hana su shiga Jami’o’in da muke da su don yin karatu.
Da aka tambaye shi ko da gaske ne karin jami’o’in na da amfani idan aka yi la’akari da kalubalen samar da kudaden da ake samu, Adamu ya bayyana cewa sabbin jami’o’in duk masu zaman kansu ne, suna da isassun kudade da za su tafiyar da su, don haka bai kamata a hana su damar samar da su ba.
Baya ga haka, Ministan ya kara da cewa, “Nijeriya a zahiri tana bukatar karin jami’o’i saboda wadanda ake da su ba su isa su dauki dukkan masu neman guraben karatu ba.”