Mataimakin ministan kula da cinikayya da masana’antu na kasar Ghana, Michael Okyere Baafi, ya ce ya kamata kasashen Afrika su dauki taron baje kolin tattalin arziki da cinikayya na Sin da Afrika karo na 3 a matsayin wata dama ta karfafa hadin gwiwa da kasar Sin domin bunkasa raya masana’antu da ababen more rayuwa.
Micheal Baafi ya bayyana haka ne ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua yayin wani taro jiya, domin yayata baje kolin tattalin arziki da cinikayya na Sin da Afrika karo na 3.
Baje kolin mai taken “ci gaba na bai daya domin makoma ta bai daya”, zai gudana ne daga ranar 29 ga watan Yuni zuwa 2 ga watan Yuli a Changsha, babban birnin lardin Hunan na tsakiyar kasar Sin.
Yayin taron da ya gudana a birnin Accra na Ghana, jami’an kasar Sin sun gabatar da manufofin zuba jari masu gwabi ga ‘yan kasuwar kasar, da fatan karfafa hadin gwiwa a tsakaninsu.
A cewar Micheal Baafi, tun bayan da yankin ciniki mara shinge na Afrika (AfCFTA) ya fara aiki a shekarar 2019, Afrika ta zama wata babbar kasuwa ga masu zuba jari na kasar Sin. Yana mai cewa idan ana son karawa nahiyar kuzari, to kamata ya yi a samu sansanin sarrafa kayayyaki karkashin yankin.
Ya kara da cewa, ya yi ammana Sinawa da mutanen Ghana za su iya hada gwiwa wajen bunkasa masana’antu a kasashen Afrika da dama.
Ya kuma bukaci kamfanonin kasar Sin su zuba jari a masana’antar samar da motoci na Afrika, inda kuma ya yi kira ga kamfanonin Ghana, su yi amfani da baje kolin wajen kulla hadin gwiwa da takwarorinsu na kasar Sin. (Fa’iza Mustapha)