Zababben Sanatan Zamfara ta Yamma, kuma dan takarar Shugabancin Majalisar Dattawa, Abdul’aziz Abubakar Yari, ya ce tsarin karba-karba na jam’iyyar APC kan mukaman shugabancin majalisar dattawa ta 10 ya ci karo da kundin tsarin mulki na 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima), hakan kuma ya saba wa ka’idar hukumar daidaito ta tarayya.
Yari ya ce, amfani da addini wajen daidaito kan raba mukaman siyasa na jam’iyyar APC sam tsarin kundin mulkin kasa na 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima) bai san da wannan tsarin ba, kundin tsarin mulkin ya baiwa hukumar daidaito ta tarayya damar kula da daidaito a kasa ba wai duba manufar addini ba.
Idan dai za a iya tunawa, a makon da ya gabata ne jam’iyya mai mulki ta amince da nada Sanata Godswill Akpabio daga (Kudu maso Kudu) da Sanata Barau Jibril daga (Arewa-maso-Yamma) a matsayin Shugaban Majalisar Dattawa da Mataimakinsa a Majalisar Dattawa ta 10 mai zuwa.
Amma, tsohon gwamnan jihar Zamfara wanda ya yi magana a ranar Talata yayin da ya kasance bakon mako na shirin gidan talabijin na Arise News Channel, mai suna ‘The Morning Show’, ya bayyana cewa tsarin karba-karba na jam’iyyar APC na zaben shugaban majalisar dattawa ta 10 sun sabawa kundin tsarin mulkin Nijeriya, kuma tsarin baiwa Arewacin Nijeriya adalci ba domin duk shugabannin bangarori uku na gwamnati ‘yan Kudu ne.