Rundunar ‘yansandan Jihar Anambra ta cafke wasu mutum biyu da ake zargi da hannu a harin da a kai kan wasu ma’aikatan ofishin jakadancin Amurka a karamar hukumar Ogbaru ranar Talata.
LEADERSHIP ta tattaro cewa gwamnatin Amurka ta ce harin bai kai ga hallaka wani Ba’Amurke ba, amma wasu daga cikin ma’aikatansu ne harin ya shafa wadanda ba Amurkawa ba.
- Na Yi Mamakin Ganawar Antony Blinken Da Tinubu -Atiku
- Na Yi Mamakin Ganawar Antony Blinken Da Tinubu -Atiku
Da ya ke magana kan wannan lamarin a ranar Alhamis, kwamishinan ‘yansandan jihar Anambra, Mista Echeng Echeng, ya ce, hadakar jami’an tsaro da suka hada da soji, ‘yansanda, sojin ruwa su ne suka mamaye wata maboyar wadanda ake zargin a yankin Ugwuaneocha da ke karamar hukumar ta Ogbaru.
Ya ce, lokacin da jami’an tsaron suka isa, sun tarwatsa maboyar. Kuma sun samu nasarar cafke mutum biyu da suke zargi wanda a halin yanzu ma suna kan fuskantar tambayoyi.
Da ya ke ganawa da ‘yan jarida a shalkwatar hukumar a Amawbia, kwamishinan ya kara da cewa, wadanda lamarin ya rutsa da su sun hada da jami’an jakadancin Amurka su biyar da ‘yansanda su hudu masu musu rakiya wanda suke kan aikin duba illar da zaizayar kasa ya yi a karamar hukumar Ogbaru.
Ya ce, suna cikin motoci biyu ne yayin da aka kaddamar da hari a kansu.
Kwamishinan ya kara da cewa bincikensu na cigaba da gudana kuma za su sanar da jama’a dukkanin abubuwan da suka tattara na bayanai a lokacin da ya dace.