Rahotanni na cewa, wasu manyan jami’an gwamnatin Amurka sun bayyana cewa, sanarwar taron kolin kungiyar G7 na bana, za ta jaddada wajabcin nuna “damuwa” kan kasar Sin, maimakon “mayar da ita saniyar ware”. Kan haka ne, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya jaddada a gun taron manema labaru na yau da kullum Jumma’ar nan cewa, abin da kasar Sin ke kawowa duniya, shi ne damammaki maimakon kalubale, kwanciyar hankali maimakon hargitsi, da inshora maimakon hadari.
Wang Wenbin ya bayyana cewa, kasar Sin na tsayawa tsayin daka kan hanyar samun bunkasuwa cikin lumana, kana tana bin dabarun bude kofa ga juna tare da samun moriyar juna. A cikin shekaru 10 da suka gabata, matsakaicin adadin gudummawar da Sin ta bayar ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya, ya zarce adadin na kasashen G7 baki daya.
Bugu da kari Wang Wenbin ya bayyana cewa, matakin da kasar Sin ta dauka na kin amincewa da shigar Taiwan cikin taron kiwon lafiya na duniya na bana, ya samu goyon baya da fahimta sosai daga kasashen duniya. (Mai fassarawa: Ibrahim)