Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya umurci duk masu rike da mukaman siyasa da su mika takardunsu na ajiye aiki daga yanzu zuwa ranar Juma’a 26 ga Mayu, 2023.
Masu rike da mukaman sun hada da kwamishinoni, masu ba da shawara na musamman, manyan jami’an gudanarwa na kamfanoni mallakar gwamnati, babban mataimaki na musamman, mataimaka na musamman, ma’aikatan hukumomin gwamnati.
- Gwamnati Mai Jiran Gado Ta Sha Alwashin Kwato Kadarorin Jama’a Da Gwamnatin Ganduje Ta Sayar.
- Tinubu Da Kwankwaso Sun Gana A Faransa
Wata sanarwa da ta fito daga babbar sakatariya a ofishin sakataren gwamnatin jihar, Bilikisu Shehu Maimota, ta fitar a ranar Litinin din nan, ta umurce su da su mika aiyukansu ga manyan sakatarori ko daraktocin gudanarwa na ma’aikatun gwamnati.
“Wannan ya yi daidai da tsarin da aka kafa domin wa’adin mulki na biyu na Gwamna Abdullahi Umar Ganduje zai cika a ranar 29 ga Mayu, 2023,” cewar sanarwar.