Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Wang Wenbin, ya ce bayan girgizar kasar da ta aukawa Afghanistan, kasar Sin ta yanke shawarar bayar da agajin gaggawa na yuan miliyan 50 ga Afghanistan, da suka hada da rumfuna da gadajen tafi da gidanka da tawul da sauran kayayyaki na gaggawa da mutanen da iftila’in ya rutsa da su ke bukata.
Ya ce an tsara kashin farko na kayayyakin zai tashi cikin jirgin da aka yi shata, a ranar Litinin, 27 ga wata. (Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha daga CMG Hausa)