Ƙungiyar ‘yan sintiri ta kasa wacce akafi sani da ‘yan banga (VGN), ta shigar da koke ga Hukumar DSS kan bukatarta na cafke wani tsohon jami’anta wanda ta dakatar mai suna Usman Mohammed Jahun.
VGN tana tuhumar Jahun ne da laifin atisayen ɗaukar ma’aikata ba bisa ƙa’ida ba da nufin zamba.
Shugaban Ƙungiyar kuma tsohon kwamandan rundunar sojojin ruwa, Umar Bakori ne ya bayyana hakan acikin takardar koken da hukumar ta ƙasa ta sanya wa hannu, wanda aka raba wa kafafen yaɗa labarai a safiyar Lahadi.
Ya ce, “hankalin ƙungiyar ‘yan banga ta Nijeriya (VGN) ya karkata kan wani mai suna Usman Mohammed Jahun, tsohon ɗan ƙungiyar da aka dakatar wanda aka yi zargin yana tantance jama’a ba bisa ƙa’ida ba tare da karɓar kuɗaɗensu da nufin shigar da su ƙungiyar VGN. Jahun ya kasance yana yayata cewa, shugaba Buhari zai rattaba wa kungiyar VGN hannu ta zama ta Gwamnati kafin wa’adin mulkinsa ya kare”
Ya ƙara da cewa, “Da fatan za ku yi amfani da bayanai masu tushe don bincike kuma a kama Usman Mohammed Jahun kafin ya ɓata sunan VGN a wajen mutane masu neman aikin gwamnati”
Wakilin mu ya tuntuɓi Usman Jahun ta wayar salula don jin ta bakin sa game da wannan zargi, inda ya amsa masa da cewa, zai neme shi.
Sai dai har ya zuwa lokacin haɗa wannan labarin, bai nemi wakilin namu ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp