Ma’aikatan lafiya a karkashin kungiyar hadin guiwa ta fannin kiwon lafiya (JOHESU) sun fara yajin aikin sai baba-ta-gani a ranar Alhamis.
Mataimakin shugaban JOHESU na kasa, Ogbona Chimela, ne ya bayyana hakan a wata ganawa da manema labarai a ranar Alhamis a Abuja.
- Masu Kwacen Waya 5 Sun Shiga Hannun Jami’an Tsaro A Kano
- Za Mu Yi Nazarin Rahoton Mika Mulki Da Ganduje Ya Ba Mu -NNPP
Ya ce: “Sakamakon nuna son zuciya da rashin nuna halin ko in kula da ma’aikatar lafiya na tarayya ne ya sanya su shiga yajin aikin.
Ya ce batun da ake takaddama a kai shi ne, “gyara tsarin albashi na ma’aikatan lafiya (CONHESS), da biyan wasu alawus-alawus ga ma’aikatan.
Don haka, ma’aikatan kiwon lafiyar, sun bukaci aiwatar tare da daidaita al’amura in har ana bukatar su koma bakin aiki.
Sun kuma bukaci amincewar ma’aikatan lafiya a cibiyoyin da ba na asibiti ba wajen biyan sabon alawus-alawus.