Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya bukaci ‘yan siyasa su gina jama’a maimakon sace dukiyoyinsu.
Ya yi wannan nasihar ne a Minna a ranar Alhamis a lokacin da ya zama shugaba a wajen taron kaddamar da zababben gwamnan jihar Neja, Mohammed Bago.
Tsohon gwamnan ya bukaci zababben gwamnan da ya maida hankali sosai a fannin ilimi da tsaro domin amfanin jihar Neja ko kuma zai yi nadama a nan gaba, ya kara da cewa jarin da ake zubawa a fannin ilimi na iya yiwuwa ba za a ga tasirinshi ba nan take amma a karshe za a ga sakamako mai dimbin yawa.
Ya kara da cewa, Bago ya zama gwamna mai taka rawar gani, dole sai ya kama aiki tukuru bayan an rantsar da shi don cigaban tattalin arziki da jin dadin zamantakewar al’ummar jihar.
Ya bayyana cewa rashin aiki da ilimi ya sa gwamnoni da dama ba su da wani abin a zo a gani a jihohinsu bayan shekaru hudu ko takwas na mulki da suka yi.