Ana sa ran alkalai guda biyar za su yanke hukuci game da zaben shugaban kasa da ya gudana a ranar 25 ga watan Fabrairu.
Kimanin masu kada kuri’a miliyan 24 ne suka hallara a rumfunan zabe sama guda 176,000 da ke fadin kasar a watan Fabrairu, domin zaben shugaban Nijeriya, amma mutane biyar ne kawai za su raba gardama a wani dakin taro da ke Abuja a watan Satumba.
Makomar zababben shugaban kasa, Bola Tinubu na jam’iyyar APC za ta ci gaba da tangal-tangal bayan an rantsar da shi a matsayin shugaban Nijeriya a ranar 29 ga watan Mayu. Zai ci gaba da zama cikin rashin tabbas har sai alkalan da za su saurari kararrakin da ke kalubalantar nasararsa za su yanke hukunci.
Korafe-korafen zabe sun kasance wani matakin dambarwa ga dimokuradiyya wanda masu rinjaye suke mulki. Zabin ‘yan tsiraru na iya daukar matsayin shawara kan masu rinjaye.
Hakan ya ba da dalilin da ya sanya miliyoyin ‘yan Nijeriya na ciki da wajen ke bibiyan shari’ar kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa da ta fara zama a Abuja.
Kotun za ta sake duba tarin hujjoji daban-daban na shari’a wadanda aka gabatar a cikin kararraki uku da ke gabanta.
‘Yan adawa sun shigar da kara na kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana.
Kotun dai na da har zuwa watan Satumba wa’adi na karshen kwanaki 180 daga watan Maris lokacin da ‘yan takarar da suka fadi suka shigar da karar, domin yanke hukuncin.
Hukuncin dai ba shi ne na karshe ba, saboda wanda bai gamsu da hukuncin ba zai iya daukaka kara zuwa kotun koli. Sai dai lauyoyin sun ce hukuncin kotun daukaka kara zai kasance tsani ga yadda za a yanke hukuncin karshe na kotun kolin, ko dai ya kasance irin daya ko kuma a samu sabani.
Ta hanyar amfani da bayanan da ake da su a bainar jama’a, ga wasu alkalai biyar wadanda za su yanke hukuncin da ake jira a watan Satumba.
Alkali Haruna Simon Tsammani
Mista Tsammani ya kasance dan asalin karamar hukumar Tafawa Belewa da ke Jihar Bauchi, shi ne shugaban alkalai guda biyar na kotun sauraron karar zaben shugaban kasa.
Yana da shekaru 63 a duniya, wanda ya kance matayi na 12 a jerin alkalan 76 na kotun daukaka kara. An dai zabe shi a wannan matsayin ne saboda kwarewarsa wanda sauran alkalai masu sauraron karar zaben shugaban kasa za su kasance a karkashinsa.
A shekarar 1983, Mista Tsammani ya halarci makarantar lauyoyi da ke Jihar Lega, kuma ya shafe feye da shekaru 40 yana aikin alkalanci. Bayan ya kammala karatun digirinsa a jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zariya a takanin shekarar 1972 zuwa 1982.
A ranar 4 ga Yulin 2020, Mista Tsammani ya zantar da hukuncin tabbatar da zaben Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello a mulkinsa na wa’adi na biyu a kotun daukaka kara da ke Abuja.
Haka kuma a watan Oktoban 2021, ya zantar da hukuncin watsi da karar dakataccen shugaban jam’iyyar PDP, Uche Secondus, har sai jam’iyyar da gudanar da babban taronta na kasa.
Shi ne alkalin daukaka kara da ya zantar da hukuncin sakin shugaban kungiyar kafa kasar Biyafara, Nnamdi Kanu daga daga gidan yari a watan Oktoban 2022.
Alkali Stephen Jonah Adah
Mista Adah ya fito ne daga karamar hukumar Dekina da ke Jihar Kogi a Arewa ta tsakiyar Nijeriya.
Shi ne mai lamba 23 a cikin jerin alkalan kotun daukaka kara, shi ne na biyu mafi girma a alkalai a kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa. A yanzu haka shi ne alkalin kotun da ke garin Asaba na Jihar Delta.
Mista Adah yana da shekaru 65 a duniya. Haka kuma ya yi karatun digirin-digirgir a fannin shari’a a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, ya kuma halacci makarantar lauyoyi da ke Jihar Legas. Ya samu saidar zama lauya tun a shekarar 1982, kimanin shekaru 41 da suka wuce.
An dai fara nada shi a matsayin alkalin babbar kotun tarayya shekaru 24 da suka gabata a ranar 12 ga Nuwambar 1998.
A kotun daukaka kara, Mista Adah ya yanke hukunci kan wani kwamitin mutum uku wanda ya tabbatar da hukuncin da aka yanke wa tsohon gwamnan Jihar Filato, Joshua Dariye, a ranar 16 ga Nuwamba, 2018. Daga baya Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi wa Mista Dariye afuwa tare da tsohon gwamnan Taraba, Jolly Nyame, bayan da kotun koli ta tabbatar da hukuncin dauri da aka yanke musu.
A watan Mayun 2019, Mista Adah ya yanke hukuncin da ya ceto tsohon Alkalin-alkalan Nijeriya (CJN), Walter Onnoghen, wanda aka gurfanar da shi a kotun da’ar ma’aikata (CCT), tare da tsige shi daga mukaminsa.
A ranar 24 ga Yuli, 2020, ya yanke hukunci kan wani kwamitin kotun daukaka kara da ke tabbatar da wanke wani dan’uwan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, Robert Azibaola, da matarsa, Stella Azibaola, da ake zargi da karkatar da kudade kimanin dala miliyan 40 na tsaro.
A wannan shekarar, a ranar 4 ga watan Disamba, 2020, Mista Adah ya jagoranci wani kwamitin alkalai da suka tabbatar da hukuncin kisa da aka yanke wa Maryam Sanda, wacce ake zargin ta daba wa mijinta, Bilyaminu Bello, wuka har lahira.
Alkali Misitura Bolaji-Yusuf
Misis Bolaji-Yusuf, mace daya tilo a cikin alkalan kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa, ta fito ne daga karamar hukumar Oyo ta yamma da ke kudu maso yammacin Nijeriya.
Mai shari’ar wacce ta kammala karatun shari’a a jami’ar Obafemi Awolowo, tana da shekaru 63 a duniya.
An nada Misis Bolaji-Yusuf a kotun daukaka kara a ranar 24 ga Maris ta 2014, kimanin shekaru tara da suka gabata, a yanzu ita ce ke matsayi na 31 a jerin sunayen alkalan kotun.
Kafin a nada ta a kotun daukaka kara, ta shafe shekaru 17 a cikin aikinta na shari’a wanda aka fara da nadita a matsayin alkalin babbar kotun Jihar Oyo a ranar 30 ga Janairun 1997.
Misis Bolaji-Yusuf ta zama alkali mafi dadewa a cikin alkalai biyar a kotun da ke sauraron kararrakin zaben shugaban kasa, inda ta shafe shekaru 26 tana aiki ba tare da samun nakasu ba.
A ranar 12 ga watan Janairun 2006, a matsayin alkalin babbar kotun Jihar Oyo, Misis Bolaji-Yusuf, ta zantar da hukuncin da ya sama wa matakin da mukaddashin babban alkalin jihar, Afolabi Adeniran ya dauka, wanda ya kai ga tsige Gwamna, Rashidi Ladoja ba bisa ka’ida ba.
Duk da cewa mukaddashin alkalin ya janye karar daga hannunta, hukuncin da ta yanke shi ne babban lamari wanda ta kai ga tsige shi, wanda kuma kotun koli ta soke shi daga baya. Kotun kolin ta mayar da Mista Ladoja a kan hukuncin da ta yanke a ranar 11 ga watan Nuwamban 2006.
An kuma ruwaito cewa ta zartar da hukunci na alkalai uku na kotun daukaka kara na Benin da suka tabbatar da zaben gwamna Godwin Obaseki a watan Yunin 2017.
Alkali Boloukuoromo Moses Ugo
Mista Ugo ya fito ne daga karamar hukumar Kolokuma/Kpokuma a Jihar Bayelsa da ke kudancin NIjeriya.
Dan shekaru 57, shi ne mafi karancin shekaru a cikin alkalan kotun da ke sauraron karar zaben shugaban kasa.
Ya dai kammala karatun lauya a jami’ar Kalaba, wanda aka nada shi alkali a kotun daukaka kara a ranar 24 ga Maris 2014, wanda a bana ya zama na tara a alkalan kotu, kuma ya kasance a matsayi na 44 a jerin alkalan Nijeriya.
Kafin zuwansa kotun daukaka kara, ya yi aiki a matsayin alkalin babbar kotun Jihar Bayelsa na tsawon shekaru takwas, tun daga nadin da aka yi masa a ranar 21 ga Maris, 2014.
Mista Ugo ya shafe shekaru 17 yana aiki a matsayin alkali, sannan kuma ya shafe shekaru 33 yana aikin lauya wanda aka fara kiransa lauya a shekarar 1990. Ya kuma halarci makarantar lauyoyi da ke Jihar Legas a tsakanin 1989 zuwa 1990.
A yanzu haka dai Mista Ugo yana aiki a sashen kotun daukaka kara na Jihar Kano, ana yawan karanta labarinsa a kafafen yada labarai.
Shigar sa cikin alkalan kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa wani muhimmin al’amari ne a rayuwarsa, inda ya kara daga darajarsa a kasar nan.
Alkali Abba Bello Mohammed
Mista Mohammed ya fito ne daga Jihar Kano, arewa maso yammacin Nijeriya, kuma shi ne na uku a cikin alkalan sauraron kararrakin zaben shugaban kasa. Ya dai kammala karatunsa ne a jami’ar Amadu Bello (ABU) da ke Zariya.
Ya kasance lauya a shekarar 1984, wanda ya zama farkon aikinsa na shari’a kimanin shekaru 39 da suka gabata.
Kamar sauran alkalan, ya halarci makarantar lauyoyi da ke Jihar Legas, domin koyon aikin alkalanci a Nijeriya.
Dan shekaru 62 da haihuwa, yana da kasa da shekaru biyu a kotun daukaka kara kamar yadda aka nada shi a ranar 28 ga watan Yuni 2021, karo na karshe da aka nada alkalai a kotun daukaka kara.
Ya kasance alkalin da ba a san shi ba, wanda a halin yanzu yana aiki a kotun daukaka kara ta Ibadan, reshen Jihar Oyo, ya kasance mafi karancin matsayi a kan kujerar kotun a tsakanin alkalan da ke sauraron kararrakin zaben shugaban kasa. Ya kasance matsayi na 71 a jerin alkalan kotun daukaka kara.
Kafin a kara masa matsayi zuwa kotun daukaka kara, Mista Mohammed ya yi aiki a babbar kotun tarayya da ke Abuja, daga shekarar 2010, inda ya shafe kimanin shekaru 10 zuwa 11.
Kasancewarsa a kotun sauraron karar zaben shugaban kasa na iya kara daga darajarsa zuwa mataki nag aba.
Har yanzu ba a ba shi wani muhimmin shar’a da aka watsa rahotannin a kafofin watsa labarai, watakila ana iya samun sunansa da yawa a cikin wasu rahotannin da suka shafi shari’o’i.