Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta ci tarar wasu mutane uku da suka shigar da kara da lauyansu miliyan 17 kan dakatar da bikin rantsar da zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
Kotun ta ci tarar Praise Ilemona, Fasto Paul Issac Audu da kuma Dokta Anongu Moses wadanda suka shigar da karar.
- Hasashe Game Da Manyan Alkalai Biyar Da Za Su Yanke Hukunci Kan Nasarar Tinubu
- Awanni 24 Kafin Rantsarwa, Shugaban Rikon Kwarya A Jihar Yobe Ya Rasu
Masu shigar da karar uku za su hada kai ne su biya zababben shugaban kasa kudi Naira miliyan 10 da kuma wani da kuma miliyan biyar jam’iyyar All APC, wadda ke cikin wadanda ake tuhuma da karar.
Lauyan masu kara, Daniel Elomah, wanda ya shigar da karar a kotu ta bayyana lamarin a matsayin abin haushi.
A zaman da aka yi a ranar Juma’a, Elomah ta roki a yafe wa wadanda ta ke karewa.
Babban Lauyan shari’a, Prince Lateef Fagbemi, SAN, wanda shi ne mashawarcin Tinubu a kan karar, ya bayar da hujjar cewa za a yi watsi da karar ne saboda masu shigar da karar uku ba su da hujjar kafawa.
Babban Lauyan ya sanar da kotun cewa babu daya daga cikin masu shigar da kara da ya halarci zaben fidda gwani da ya samar da zababben shugaban kasar.
Fagbemi SAN ya kuma kara da cewa masu shigar da kara sun cin zarafin kotu ta hanyar yawan shari’o’in da suke yi wa Tinubu da APC a kotuna daban-daban ba tare da wani dalili na daukar mataki ba.
Hukuncin babbar kotun tarayya ya zo ne sa’o’i 24 bayan kotun daukaka kara da ke Abuja ta ci tarar miliyan 40 kan tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben 2019, Cif Ambrose Albert Owuru, wanda shi ma ya nemi a dakatar da rantsar da Tinubu.