Kotun koli ta yi fatali da karar da jami’yyar PDP ta shigar a gabanta kan bukatar da a soke takarar zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Tinubu da zababben mataimakin shugaban kasa sanata Kashim Shettima a matsayin ‘yan takarar jami’yyar APC.
Kotun a karkashin jagorancin Alkalai biyar, ta yanke wannan hukuncin ne a yau Juma’a a kan karar da PDP ta shigar, inda kotun ta ce PDP ba ta hurumin shigar da wannan karar tun da ita ba mamba ba ce a Jam’iyyar APC.
- Dalibai Sun Bukaci Tinubu Da Gwamnoni Da Su Kula Da Sha’anin Tsaro, Ilimi Da Wutar Lantarki
- Mika Mulki: Yadda Buhari Ya Fara Damka Ragamar Shugabancin Nijeriya A Hannun Tinubu
PDP dai, ta yi ikirarin cewa, zabo Shettima a matsayin mataimakin Tinubu, ya saba wa sashe na 29, daya a cikin baka da sashe na 33, 35, 84 daya a cikin baka da kuma biyu a cikin baka na dokar zabe ta shekarar 2022 da aka sabunta.
PDP ta kuma yi korafin cewa, zabo Shettima don ya tsaya takarar mataimakin shugaban kasa da kuma takarar kujerar sanata ta Borno ta tsakiya a lokaci daya, hakan ya saba wa doka.
A nasa bangaren, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu, Alh. Atiku Abubakar, ya mayar da martani kan watsi da karar da jam’iyyar ta shigar kan rashin dacewar takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar APC, Kashim Shettima.
Atiku ya rubuta: “Kotun koli ta yi watsi da karar @OfficialPDPNig ba koma baya bane ga neman adalcina. Tawagarmu ta lauyoyinmu sun shirya tsaf don tabbatar da cewa zaben na ranar 25 ga watan Fabrairu cike yake da magudi, bai bi ka’idojin tsarin mulki da ka’idojin zabe na Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa ba.
“Yakin tabbatar da dimokuradiyya da kuma dora sabon tsari na bunkasa ci gaba da ci gaba a Nijeriya shi ne wanda na sadaukar da dukkan abin da na yi a kai, wanda kuma ban shirya tafiya a kai ba a wannan lokaci da al’ummarmu ke cikin tsaka mai wuya.
“Ina kira ga magoya bayana da su yi hakuri su kuma gudanar da harkokinsu cikin lumana yayin da muke gudanar da kararmu a gaban kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa -AA.”