Wasu mutum biyar da ake zargin ‘yan tawayen Oodua ne da suka kwace ragamar gudanar da gidan rediyon Amuludun 99.1 FM da ke Ibadan a safiyar ranar Lahadi sun fada komar jami’an tsaro.
Tashar wacce mallakin gidan rediyon gwamatin tarayya (FRCN) ce, a cewar rahotonnin an kwace ragamar tafiyar da ita tashar ne da misalin karfe shida na safiyar ranar Lahadi.
- Sabo Ahmad Kafin-Maiyaki: Bankwana Da Hazikin Dan Jarida, Abokin Aiki
- Gwaman Zamfara Ya Nemi Afuwa Kan Tashar NTA Da Gidan Radiyon Pride
Wadanda ake zargin sun yi dirar mikiya gidan rediyon dauke da nau’ikan layu daban-daban.
‘Yan tawayen suna ikirarin cewa, “Kasar Oodua ta samu domin ta kafu da kafafunta” “Yarbawa yanzu ba su karkashin gwamnatin Nijeriya ”
“Kwanan nan majalisar dinkin duniya za ta ayyana kasar Oodua” da dai sauran batutuwan da kai tsaye ke nuni da kalamai ne na taware.
Babban manajan gudanarwa na gidan rediyon, Mista Stephen Agbaje, ya tabbatar da faruwar lamarin.
“Wasu kungiyar ‘yan aware sun zo wajajen cikin dare, sun kwace ikon tafiyar da gidan rediyon, amma yanzu lamarin ya dawo daidai domin jami’an tsaro sun yi gaggawar kawo dauki inda suka samu nasarar kwato gidan rediyon, kuma an kama wasu ma kan batun,” Cewarsa.