Madabba’ar adabi ta kwamitin tsakiya na JKS ta wallafa littafin dake kunshe da jerin mukalolin shugaba Xi Jinping, sakatare janar na kwamitin kolin JKS, game da dogaro da kai da samun karfi a fannin kimiyya da fasaha.
Tun bayan taron wakilan jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin karo na 18 a shekarar 2012, kwamitin kolin jam’iyyar karkashin jagorancin Xi Jinping ke bayar da muhimmanci matuka ga kirkire-kirkire a fannin kimiyya da fasaha, wanda ya kai ga samar da manyan nasarori da sauye-sauye a bangaren ayyukan da suka shafi kimiyya da fasaha a kasar.
Mukalolin na Xi Jinping sun bayyana muhimman manufofi da ayyuka da matakai da abubuwan da ake bukata na inganta kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha. Sun kuma kasance masu muhimmanci wajen jagorantar kasar Sin, ta yadda ta zama jigo a bangaren kimiyya da fasaha da bunkasa dogaro da kanta da kara mata karfi a fannin da ma inganta ci gaba mai inganci da ta samu.(Fa’iza)