Gwamnatin jihar Zamfara ta amince al’ummar jihar da su yi amfani da makamai da Bindigogi wajen kare kansu da yaki da ‘yan bindiga.
Dangane da yadda ake samun yawaitar hare-hare a jihar, hukumomin Zamfara sun umurci kwamishinan ‘yan sandan da ya baiwa wadanda suka cancanci rike makamai lasisin rike bindiga.
Gwamnati ta ce a shirye ta ke ta samar da makamai ga jama’a musamman manoma domin kare kansu.
“Bayan karuwar ayyukan ‘yan bindiga a sassa daban-daban na jihar, kudurin gwamnati na tabbatar da ingantaccen tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar, musamman a wannan lokacin damina, gwamnati ta yanke shawarar daukar wasu matakai don magance matsalar yadda hare-haren ‘yan Bindiga ke kara ta’azzara a baya-bayan Na yadda ake sace-sacen jama’a da basuji ba su gani ba.
“A yanzu gwamnati ta amince al’ummar jihar su mallaki bindigogi don kare kansu daga ‘yan bindigar, kamar yadda gwamnati ta umurci kwamishinan ‘yan sandan jihar da ya ba da lasisi ga duk wanda ya cancanta kuma yake son samun irin wadannan bindigogi don kare kansa.
“Gwamnati a shirye ta ke ta taimaka wa al’ummarta, musamman manoman wajen samar musu da makamai da bindigu don kare kansu.
“Gwamnati ta kammala shirin raba bindigu 500 ga kowace masarautu 19 da ke jihar domin rabawa masu son kare kansu.”
Daily trust ta rahoto cewa, Gwamnatin ta kuma kafa wani kwamiti don Tsare-tsare da tabbatar da aiwatar da matakan mallakar bindigun yadda ya kamata. Rahoton