‘Yan awaren Biyafara 30, sun fada a komar ‘yansanda a Jihar Enugu.
Jami’an sun kama su ne a lokacin da suke kan guanar da bikin murnar ranar Biyafara a Jihar Enugu.
- Maganar Tarkon Bashi Ta Nuna Rashin Karfin Gwiwar Kasashen Yamma
- Pochettino Ya Karbi Aikin Horar Da Chelsea
Wadanda aka kama din, sun kasance ‘ya’yan kungiyar ‘yan Biyafara ne bangaren BZM.
Wata majiya ta ce, an kama su ne da misalain karfe 11 na safiyar yau Talata, inda aka dauke su zuwa hedikwatar ‘yansandan jihar.
Leadership ta tuwaito cewa, sun taru ne a titin Layout da ke Enugu a yayin da suke daf da fara yin tattaki.
A cewar majiyar, ‘yan kungiyar ta Biyafa sun fito yin tattakin nasu ne, dauke da tutar Biyafara da ta kasar Israila da kuma ta kasar Amurka.
Sun kuma fito tattakin na su, dauke da wasu alluna da ke dauke da sakonni.
Majiyar ta kara da cewa, a lolacin da suke daf da fara yin tattakin ne, sai motocin ‘yansanda kirar Hilux guda biyar suka iso wajen suka lama su,inda majiyar ta ce, sun kasance bas a dauke da wasu makamai tare da su.
Kakakin rundunar ‘yansandan jhar DSP Daniel Ndukwe ya bayyana cewa, bai samu bayanai kan kamun ba.