A bana aka cika shekaru goma da gabatar da manufar gaskiya, kusanci, da sahihanci da maanar adalci da faida a hadin gwiwar Sin da Afirka, da cika shekaru 60 da kafuwar kungiyar tarayyar Afirka.
A halin da ake ciki, an gudanar da taro karo na 12 na dandalin masana tsakanin Sin da Afirka a birnin Jinhua na lardin Zhejiang dake kudancin kasar Sin a jiya Talata ranar 30 ga wata.
Taron mai taken Farfado da hadin gwiwar Sin da Afirka na shekaru 100” ya samu halartar jami’an gwamnati, da masana, da walikan kafofin yada labarai da ‘yan kasuwa daga kasashe 42 da suka hada da Sin da Najeriya da Afirka ta Kudu da Tanzaniya da sauransu.
A jawabinsa yayin bude taron, wakilin musamman na gwamnatin kasar Sin mai kula da harkokin Afirka Liu Yuxi ya bayyana cewa, yanzu kasar Sin ta fara sabuwar tafiya ta zamanantar da kasa mai ra’ayin gurguzu ta zamani a dukkan matakai, kuma tana kan gaba wajen cimma burin kafa kasar Sin mai tsarin gurguzu ta zamani mai wadata, bisa tsarin demokuradiya, wayin kai da kuma jituwa nan da shekara 2049, wato yayin bikin cika shekaru 100 da kafa jamhuriyar Jamaar Sin.
A nasu bangaren, kasashen Afirka na hanzarta aiwatar da yunkurin neman dunkulewar nahiyar waje guda, da kokarin hada kai don neman ci gaba da farfadowa. Dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka ta shiga matakin samun ci gaba mai inganci a dukkan fannoni cikin hanzari.
Darektan cibiyar nazarin kasar Sin dake Najeriya, Charles Onunaiju, ya yi imanin cewa, kasashen Afirka da Sin suna da damuwa iri daya a bangarori da dama, kuma karfafa hadin gwiwa da muamalar juna tsakaninsu, zai amfanawa kasashen nahiyar. A hannu guda kuma, ya dace nahiyar ta koyi kwarewar da kasar Sin ta samu a fannin rage radadin talauci. (Mai fassara: Bilkisu Xin)