Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau Laraba cewa, Sin tana goyon bayan gwamnatin kasar Mali a kokarin da take na yaki da ta’addanci da tabbatar da tsaron kasa.
Mao Ning ta bayyana haka ne yayin da aka yi mata tambaya game da wani rahoto da aka fitar dake cewa, sojojin kasar Mali da sojojin haya na kasashen waje sun keta hakkokin dan Adam a yayin aikin yaki da ta’addanci a Moura.
Mao Ning ta kara da cewa, Sin ta kasance mai bayar da shawara ga bangarori daban daban da su tattauna tare da hada gwiwa da juna, kana ba ta amince da tsoma baki cikin harkokin cikin gidan sauran kasashe da sunan kare hakkin dan Adam ba. (Zainab)