Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar ya shawarci Kamfanin Talabijin na Qausain TV da ya rubanya kokarinsa wajen isar da sako ga al’umma.
A ziyarsar da Qausain TV karkashin jagorancin Shugaban Tashar, Nasir Musa Albanin Agege a fadar Sarkin Musulmin, ta kunshi wasu daga cikin shugabannin Kamfanin da suka hada da Auwal MB, Hashim Abubakar Musa, Khalifa Muhammad Babandede da kuma Hassan Haruna.
Bayan kyakkyawar tarba da tawagar ta samu, kazalika Sarkin Musulmin ya bukaci Qausain TV da ya ci gaba da aiki tukuru bisa kwarewa da sanin makamar aiki kamar yadda aka san shi wajen wayar da kan al’umma da ilmantar da su a yayin shirye-shiryensu.
Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar ya kuma yaba da yadda tashar ke yada shirye-shiryenta a bisa harsuna guda uku da suka hada da Turanci, Hausa da kuma Larabci.
A cikin jawabinsa a yayin ziyarar, Shugaban Kamfanin Qausain TV, Alhaji Nasir Musa Albanin Agege ya gode wa Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar bisa shawarwarin da ya ba su da kuma kyakkyawan tarbar da suka samu.
Ya Kuma kara da cewa, “za mu fara aiki da shawarwarin da suka fito daga uba kuma jagora anan take wajen yada shirye-shiryenmu a kowane lokaci”
Kazalika tawagar karrama Mai Alfarma Sarkin Musulmin da lambar yabo sannan ta mika masa kyautar hoton girmamawa na gilashi wanda je dauke da hoton Sarkin Musulmin.
Daga karshen tawagar ta samu damar yin hoto na jam’i tare da Mai Alfarma Sarkin Musulmi da wasu daga cikin ‘yan majalisarsa.