Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Kasa (NAHCON) ta bai wa mahajjatan Jihar Jigawa, tabbacin yin jigilarsu zuwa kasa mai tsarki lafiya.
Shugaban hukumar, Alhaji Zikrullah Kunle Hassan, a wata sanarwa da mataimakiyar daraktar harkokin jama’a ta NAHCON, Fatima Sanda Usara ta sanya wa hannu, ta ce an kammala shirye-shiryen gyara duk wani jinkiri ko soke jirgin da zai kawo cikas ga jigilar maniyyata cikin sauki zuwa Saudiyya.
- Majalisar Dokokin Filato Ta Dakatar Da Shugabannin Kananan Hukumomi Da Kansiloli
- Yanzu-yanzu: Tinubu Na Ganawa Ta Farko Da Shugabannin Tsaro
Jirgin da NAHCON ta samu kwangilar jigilar alhazan Jigawa 454 zuwa kasar Saudiyya ya yi saukar gaggauwa a filin Malam Aminu Kano sakamakon samun matsala.
Shugaban Hukumar NAHCON, yayin da yake tabbatar da faruwar lamarin ya haifar da tsaiko, ya ce an magance matsalar.
A halin da ake ciki, jigilar maniyyata aikin Hajji ta 2023 daga Nijeriya ya shiga rana ta bakwai.
Idan za a iya tunawa, domin gaggauta jigilar dukkan maniyyatan Nijeriya da ke da niyyar zuwa aikin hajjin bana, NAHCON ta kara yawan jiragen da za su yi aiki.
Ya zuwa yanzu, alhazan Nijeriya 14,188 suna cikin koshin lafiya a Madina sannan kuma adadin jiragen da ke jigilar maniyyata zuwa kasar zai karu nan da kwanaki biyu saboda an umarci maniyyatan da su kasance cikin shiri a kowane lokaci don tashi zuwa Saudiyya.
A ranar Juma’a ne rukunin farko na alhazan Nijeriya za su mamaye Makkah bayan shafe kwanaki takwas a Madina.