Ba jimawa da kammala zabukan kujerun gwamnoni cikin wannan Kasa, duba da irin dalar basukan gida da na daji da sabbin zaba6bun gwamnoni za su gada daga gwamnonin da za su mika musu mulki a karshen Watan Mayun wannan Shekara ta 2023, sai aka rika yin kacibis da alkaluma gami da muryoyin masana tattalin arzikin Kasa da sauran masharhanta daga mabanbantan sakuna da lungunan wannan Kasa, na ta baje kolin hasashensu da tsinkayensu game da wadancan gadaddun basuka, daga gwamnoni masu barin gado, zuwa ga gwamnoni masu jiran gado.
Hakika masana da masharhanta sun barje guminsu na kalubalantar jerin gwanon basukan gida da na ketare da ake kan yin tozali da su, daga akalla jihohi 17 da sabbin zaba6bun gwamnoni ne za su karbi ragamar tafikad da su bayan rantsuwa. Suma sauran jihohin Kasar, ba kanwar lasa ba ne wajen hadidiyar basukan. Sai dai akasin wadancan jihohi 17, sauran jihohin, za a danganta tuhumar ciwo basukansu ne bisa wuyayen gwamnonin nasu, tun da suma sun taka mugunyar rawa ainun wajen ciwo basukan a lokacinsu. Shi kuwa sabon gwamna ko a ce sabbin gwamnoni, sun taka sawun barayi ne, don ba su hau kan kujerar mulkin jihar ba, ballantana a kwakwalo irin nasu laifukan game da yin lallaftun wadancan miyagun basuka bisa wuyayen al’umarsu.
Sabon gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, da ake wa lakabi da Abba Gida Gida, na daga ‘yan sawun gaba cikin wadancan sabbin gwamnoni, wadanda suka fara numfasawa cikin kuncin takurarren numfashi game da tsirin basukan da gwamnonin da za su gada suka dankarawa jama’ar jihar tasu. Bashin gida kawai, Abba Gida Gida zai gaji bashin zunzurutun kudade ne har kimanin naira miliyan dubu dari da ashirin da biyar da ‘yan kai (N 125, 186, 662, 228. 72).
Ba ya ga wancan taragon bashi na gida, AKY Kano, zai sake gadar bashi na ketare, wanda ya tunkuyi zunzurutun mazajen kudade har kimanin dalar Amurka na gugar dala, har dala biliyan dari da tara da ‘yan kai ($ 109, 422, 176. 85). Mai yi wa, ganin wannan shuri ko a ce tsibiri na basuka, ga dukkan alamu, sune suka hana sabon gwamna Gida Gida runtsawa, awanni kalilan bayan ya lashe zaben kujerar gwamnan Kano, a karkashin jam’iyyar NNPP. An jiyo mai girma sabon gwamna na jan-hankali ne za a ce, ko jan-kunnen duk wasu mutane da ke kankajeren son kara laftawa al’umar jihar Kano sabon bashi, ta hannun gwamna mai barin gado Ganduje;
“…I will not honour any loan given to Ganduje after 18th March, 2023”.
Abba Gida Gida
A cikin harshen Hausa, wancan turanci da sabon gwamnan na Kano ya furzar cikin kaduwa da bacin rai, na nufin, “Zan yi hannun riga da duk wani bashi da za a bai wa gwamna Ganduje, bayan 18 ga Watan Mac, na Shekarar 2023)”. A takaice a nan, zaba6ben gwamna Abba Kabir Yusuf na nufin cewa, bayan 18 ga wancan Wata da aka ambata, duk wanda ya yi kirinkin bai wa gwamna mai barin gado Ganduje wani bashi, to fa sabuwar gwamnatinsu ta NNPP ba za ta bata lokaci ba wajen tunanin biyan wadannan basuka ba !!!.
A ranar da ya rage mintoci a rantsar da sabon gwamnan na Kano AKY, an ji shi yana fadin cewa, cikin kundin mulkin jihar da suka karba daga gwamnati mai barin gado ta Ganduje, sun iske wani irin tulin bashi da ake bin jihar ta Kano, wanda har suka kere tsabar kudi sama da naira miliyan dubu dari biyu da arba’in (N 240bn). Babu shakka wannan ruguntsumin taragon basuka, sun kidima Abban, ya kasa zaune balle tsaye, a karshe dai ya lashi takobin bincikar wadannan madudan basuka da aka gadarwa da gwamnatinsa;
i- Ta yaya ne ma aka ranto wadancan basuka?
ii- Mene ne gaskiyar abin da aka aikata da kudaden?
iii- Shin, babu wani wuru-wuru ko kuskunda cikin mu’amalar wadancan kudade na malala gashin tinkiya da aka ranto?
Lokaci ne kadai zai iya ba da amsar abin da zai faru tsakanin gwamnatin Abba da ta Ganduje game da batun tsirin basukan da akasarin jama’a ke kallo da wata annobar da ta yi silar karya tattalin arzikin Nijeriya karkashin wannan Jamhuriyar Siyasa ta Hudu da ta faro daga Shekarar 1999 zuwa yau (2023).
Ba sabon gwamna Abba ne kadai ya bara ba, game da tukunyar bashin da ke zabalbala a jiharsa ta Kano, sabon gwamnan Zamfara, Dauda Dare, ma da ya sami nasarar hambarar da gwamnatin Bello Matawalle, ya biyo sawu, inda yake kukan cewa, ya zo ya iske asusun jihar ta Zamfara an yi masa mugun ta’annati, an yi masa karkaf, babu kudi babu alamunsu ciki. Uwa uba kuma, an ciwowa jihar ta Zamfara wani irin mamakon tulin bashi iya wuya.
Basukan Na Kassara Kasashen Duniya Ne
Yayinda wasu Kasashen Duniya irin su Amurka ke morar basukan da suke ciwowa mutanensu, sai lamarin ya zamto akasinsa ne ke faruwa a akasarin kasashenmu na Afurka, cikinsu kuwa har da Nijeriya. A Kasashe irinsu Amurka, a kan sa irin wadancan basuka ne cikin wasu sha’anonin da za su bunkasa ne, har su sami sukunin biyan irin wadannan basuka. Misali, sanya kudaden cikin sabgar hannun jari, ko cikin wasu aikace aikacen da za su matso makudan kudade, misali, cikin sabgar lafiya, ko ilimi, ko noma da sauransu. Ta tabbata cewa, a harkar noman lemon zaki “Orange” kawai a Shekara a Amurka, a na samun kudaden shigar da suka kere adadin kudin shigar da Nijeriya ke samu a harkar man fetur a Shekara.
Babban abinda ke bai wa kowace Kasa a Duniya fursar biyan kudaden da ta ranto, bai wuce a sanya wadannan basuka cikin wasu wuraren da za su haihu, a sami ribar da za ta taimaka zuwa ga biyan bashin. A fili yake cewa, a duk sa’adda aka wayigari wata Kasa a Duniya ta yi hani’an da irin basukan da ‘yan koren jari hujja ke badawa, irinsu Bankin Ba Da Lamuni na Duniya (IMF), koko Bankin Duniya (World Bank), kuma Kasar ta gaza biya ko ta durkushe, ko tana neman durkushewa, abin da ke biyo baya shi ne, wasu tsauraran ka’idoji ne da wasu sharudda, wadanda za su kara burkuma wannan Kasa cikin bala’i da masifar kangi na tattalin arziki. Akwai misalai birjik cikin Duniya, inda za a sami jerin Kasashen da suka gwammace ma ba su karbi irin wadancan basuka ba. Idan haka batun yake, su Abba na Kano da Dauda na Zamfara, kukansu da kuma kalubalensu ga tsoffin gwamnonin jihohinsu game da mas’alar bashin na bisa tafarki ne.
Yadda IMF Da World Bank Suka Kassara Zambia
A cikin 1980s, lokacin da Kasar Zambia ke cikin haiyacinta, rayuwa na gudana be gwanin ban sha’awa, ga tallafin gwamnati a muhimman bangarorin rayuwar jama’ar Kasa, ilmin firamare da sabgar lafiya duka kyauta ne a Kasar, karkashin mulkin shugaba Kenneth Kaunda. Ga daruruwan kamfanonin gwamnati birjik a Kasa. Ga masakun saka kayaiyaki na gida gwanin ban sha’awa, a na ta kan buga harkokin samun kudade cikin rufin asiri da walwala. Kwatsam, sai farashin man fetur ya yi gwauron tashi a Duniya, sai kuma farashin ma’adinin tagulla ko a ce jan-karfe “Copper–(kofa)” ya karye warwas! Kofa, na daga manyan ma’adinai da ke samarwa da Kasar ta Zambia mamakon kudaden shiga, saboda durkushewar farashin, sai aka wayigari labari ya sha banban!
Cikin kankanin lokaci, sai abubuwa suka canja canjawa a Kasar ta Zambia, babu makawa sai bukatar yin rancen kudi daga ketare ta kama su. Da ma masana na yin nuni da cewa, daga lokacin da Kasa ta wayigari kudaden shigarta suka yi kasa ainun, hakan na tilasa ta ne zuwa ga rantar kudi. Cikin wata hira da manema labarai, shugaba Kaunda ke cewa, yanayi da yanzu ya kama mu, na, dole sai mun ranto kudi daga waje, sai dai, na tuntubi Bankin ba da lamuni da kuma Bankin na Duniya game da shin, ko za mu iya samun bashin kudi daga gare su? Sun amsa min, da me zai hana?.
Bugu da kari, sun yi min alwashin cewa, babu shakka farashin kofa zai sake dagawa ba da jimawa ba. Sai dai ta tabbata cewa farashin na kofar maimakon yai kasa, sai ma kara sama ne yake yi, ba kamar yadda suka lasa masa zuma a baki ba (Analysis, June, Bol. 1 No 1, 2002 : 36).
Da lamura suka ci gaba da kwabewa a Kasar ta Zambia, bayan ciwo wadancan basuka, a karshe dai jama’ar Kasar ne suka kayar da gwamnatin Kaunda a zabe, cikin Shekarar 1991, tare da mayegurbinta da dan gwagwarmaya Frederick Chiluba, ba don komai ba, sai don a sami saukin kuncin rayuwa. Amma Ina! Sai ma wani irin curin bashin ketare ne ke neman zame musu dan-zani. Ya faru zuwa cikin Shekarar 2000, an wayigari ne a na bin Kasar Zambia zunzurutun kudade har kimanin dalar Amurka biliyan shida da digo shida ($ 6.6bn).
Dole sai da Zambia ta rika bi tana janye tallafinta daga muhimman bangarorin rayuwar jama’ar Kasa. An janye tallafin ilimin firamare kyauta, kuma an janye ma batun lafiya kyauta, saboda irin kaburin da bashin ya yi cikin Kasar kan a farga!. A dai cikin Shekarar ta 2000, gwamnatin Chiluba, ta cefanar da sama da kamfanoni mallakar gwamnatin Kasar sama da guda dari uku (300). Sannan, a hankali a hankali, hatta wuraren ma’adinan Kasar ma gwamnati ta sayar. Kuma aka wayigari, abinda gwamnati ke kashewa a harkar karatun firamare, sai ka ninka shi sau uku ne zai kai ga adadin kudaden da gwamnati ke bayarwa wajen biyan bashi a Shekara.
Shirin Ta Da Komada Na SAP “Structural Adjustment Program” A Nijeriya
Ba Zambia kadai ba, duk Kasar da tulin bashin ketare yai mata katutu ta ci gaba da hadiya shan kai, ba tare da a na sanya bashin cikin aiyukan da za su haihu ya biya kansa ba, abu na gaba da zai biyo baya shi ne, al’umar Kasa su fara dandanar kudarsu, da sunan hanya daya tilo da za a bi, don ganin an sauke wancan nauyin bashi da ya jima da danne makogwaron Kasar. Sau da yawa za a iske cewa, Turawan Yamma ne ke zuwa da irin wancan zaurance na tursasa jama’ar Kasa cikin wani sabon yanayi na kangin rayuwar.
Lokacin da kaburin basukan ketare da shugaba Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) ya ciwowa wannan Kasa tamu ta Nijeriya, sai hakan ya tilasa shi zuwa ga dabbaka irin wadancan matakai na janye tallafin gwamnati daga al’umar Kasa.
Lokacin da gwamnatin IBB ta zo da manufar ta da komadar tattalin arzikin Kasa na SAP, sai ya kasance saboda irin tsinkayen azabtuwa da jama’ar Kasa za su yi a sanadiyyar tsarin, sai aka rika samun jajirtattu ‘yan gwagwarmaya daga mabanbantan sako da lungu na Kasar, suna masu raddi gami da kausasa adawa ga tsarin na SAP. Duk kuwa da irin wannan soke soke da ake yi wa manufar ta SAP, hakan bai sanyaya gwiwar gwamnatin IBB ba, na ta janye manufar, maimakon haka ma, sai gwamnati ta rika bi kwararo kwararo tana kamewa tare da garkame mutanen da ke yin raddi ga manufar a gidajen yari na wasu Watanni.
A karkashin manufar SAP, akwai batun janye tallafin gwamnati daga muhimman abubuwa irinsu man fetur, harkar gona, harkar lafiya, tare da sayar da kamfanoni mallakar gwamnati ga ‘yan kasuwa, da sauran tsarabe tsarabe!