ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, June 15, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ta Ya Ake Gudanar Da Nagartacciyar Rayuwa?

by Sulaiman Bala Idris
1 year ago
Rayuwa

A wannan makon ina tafe ne da wata ‘yar muhawara dangane da ‘ingantacciyar rayuwa’, ta ya ya mutum zai gudanar da ita? Kuma ta wacce hanya a ke gane rayuwa ta-gari.

An dade ana samun takaddama dangane da al’amarin nagartacciyar rayuwa. wannan ne ma ya sa wasu masana a fannonin ilimi mabambanta suka yi ta tafka muhawarori dangane da yadda ya kamata mutum ya samarwa da kanshi nagartacciyar rayuwa.

  • Manchester Ta Kai Zagayen Semi Final A Europa Bayan Doke Lyon
  • Sin Da Malaysia Za Su Samar Sabbin Shekaru 50 Masu Muhimmanci Na Dangantakar Kasashen Biyu

Wannan muhawara ce mai muhimmancin gaske musamman bisa la’akari da yadda a kullum mutane ke kuskurewa kan abin da ake nufi da ‘abu na nagari’.

ADVERTISEMENT

Da farko dai kafin a fara magana a kan yiwuwar kasantuwar wani abu nagari ne ko akasin haka, sai ya zama cewa al’ummar da za a yi wannan tantancewa cikinta al’umma ce wacce ta ke tafiya akan tsari, kuma tana kumshe da dokoki wadanda da su ne ake hukunci.

Wasu daga cikin masana sun tafi ne akan cewa mutane ne ke da ikon fayyacewa tsakanin abu mai kyau da mara kyau, don haka babu wata doka da za ta iya tabbatar da kyawun abu ko rashin kyawunsa.

LABARAI MASU NASABA

Yayin Da Dangote Ya Bayyana A Ganawar Neman Aiki

A Karshe Jamilu Gwamna Ya Samu Babbar Damar Yin Takara

Masu wannan fahimta sun yi imanin cewa duk lokacin da mutum ya ji baya son wani abu to a wurinshi wannan abin ba mai kyau ba ne. Haka nan kuma duk lokacin da mutum ya ji cewa ga wani abu amma shi ne ya kwanta mashi, toh wannan abin shi ne mai kyau.

Babban misalin da wadannan masu ra’ayi suke jaddadawa da nanatawa a kullum shi ne cewa a lokacin da mutum ya yi tsammanin cewa wani abu na da kyau a ra’ayinshi, to idan ya je cikin wata al’ummar zai tarar da cewa wannan abin barna ko wani abin ki. Misali da shan giya, caca da sauransu.

Da irin wannan nazari ne aka samar da mafi shaharan nazariyyar nan ta NIHILISM, wanda ya zo da wasu ‘yan sauye-suye. Fahimtar ta Nihilism ta ce, sam babu wata doka da za ta iya bambancewa tsakanin abu mai kyau da mara kyau. Don haka ta hanyar ra’ayi da mahangar mutum ne kawai zai iya bambancewa tsakanin mai kyau da marar kyau.

Masu fahimta irin ta Nihilism sun tafi a kan cewa, dabi’ar mutum da yanayin mu’amalarsa da mutane ne kadai za ta iya ayyana nagartacciyar rayuwa ya ke yi ko akasinta. sannan kuma zantukan yabo ko zagi daga makusantan mutum su ma za su iya fayyace irin rayuwar da ya ke yi, ma’ana, abubuwan da suke fadi a kan shi.

Kowanne mutum yana dauke da wasu nauyayen abubuwa na irin dabi’un da ya kamata ya nunawa makusantanshi. Misali da akwai hakkoki na dabi’a da su ka wajaba akan shi wadanda da su ne zai mu’amalanci iyayensa. Haka nan shugaba akwai dabi’o’in da su ya kamata ya mu’amalanci mutanen da ya ke shugabanta.

Bayan samuwar wannan fanni na Nihilism, wanda shi ma ya zo da gudummawarsa dangane da yadda mutum zai gabatar da nagartacciyar rayuwa, sai masanin falsafa Plato ya bulla da sabon nazari wanda kaitsaye ya ke kalubalantar tushen nazariyyar Nihilism din. nazarin na shi ne ya yi kaurin suna har a ke yi masa lakabi da PLATONISM.

Plato cewa ya yi bayani kan wata babbar hanya da mutum zai bi ya gudanar da nagartacciyar rayuwa, inda a takaice ya ce, ‘Mutum ya nemi ilmi’. Ya ci gaba da cewa, a dai dai lokacin da mutum ya samu ilmi ya fahimci me ake nufi da nagartacciyar rayuwa, lallai babu wani abu da zai hana shi bin wannan hanya.

Plato ya ce aikata alfasha da masha’a duk suna aukuwa ne saboda karancin ilmin mai aikata su. Idan mutum ya fahimci ga gaskiya, ita zai bi domin gudanar da nagartacciyar rayuwa.

An zargi wannan nazarin da cewa, ta ya ya mutanen da ke da mabanbantan fahimta za su iya yin ilmin da za su yi nagartacciyar rayuwa? Sai ya ci gaba da bayanin cewa mutum duk ilminsa ba zai iya gano yadda ya kamata ya yi rayuwa ta gari ba, har sai ya samu horo na musamman dangane da abin da ake nufi da abu mai kyau da mara kyau.

Mutumin kuma da bai da kwakwalwar da za ta iya fahimtar karatu sai ya rika koyi da wadanda su ke da ilmi da horon gudanar da rayuwa mai kyau.

Plato ya ce, lura da tarbiyyar yara tana da muhimmanci wurin basu horo da ilmi, wanda kuma hakan zai sa su samu halayen kwarai da dattako. Yana da kyau al’umma ta yi kokarin ganin cewa wadanda ke mulkarsu (shugabanni) mutane ne masana, masu halin dattako da natsuwa da zurfin ilmi.

Lokacin da nazariyyar Platonism ta bayyana ta zama tamkar kishiya ga Nihilism. Domin kai tsaye nazarin ya yi dirar mikiya ne akan Nihilism da ra’ayoyinsa. kuma wannan tunani na Platonism ya samu karbuwa dari bisa dari a falsafar addinai. Sai dai wasu ‘yan bambance-bambance da ba za a rasa ba, da kuma gyare-gyare.

Rayuwa
Sulaiman Bala Idris
+ postsBio
  • Sulaiman Bala Idris
    https://hausa.leadership.ng/author/sulaiman-bala-idris/
    ‘Symbolic Interactionism’:Sabuwar Makaranta A Kimiyyar Zamantakewa
  • Sulaiman Bala Idris
    https://hausa.leadership.ng/author/sulaiman-bala-idris/
    Hayaniya ‘Yar Facebook!
  • Sulaiman Bala Idris
    https://hausa.leadership.ng/author/sulaiman-bala-idris/
    Mummunan Zato
  • Sulaiman Bala Idris
    https://hausa.leadership.ng/author/sulaiman-bala-idris/
    Me Ake Nufi Da Ado? 

MASU ALAKA

Yayin Da Dangote Ya Bayyana A Ganawar Neman Aiki
Bakon Marubuci

Yayin Da Dangote Ya Bayyana A Ganawar Neman Aiki

June 12, 2026
A Karshe Jamilu Gwamna Ya Samu Babbar Damar Yin Takara
Bakon Marubuci

A Karshe Jamilu Gwamna Ya Samu Babbar Damar Yin Takara

June 12, 2026
‘Symbolic Interactionism’:Sabuwar Makaranta A Kimiyyar Zamantakewa
Bakon Marubuci

‘Symbolic Interactionism’:Sabuwar Makaranta A Kimiyyar Zamantakewa

June 5, 2026
Next Post
APC Ta Gaza Gudanar Da Taron NEC Cikin Shekaru Biyu – PDP Ta Zarge Su

APC Ta Gaza Gudanar Da Taron NEC Cikin Shekaru Biyu - PDP Ta Zarge Su

LABARAI MASU NASABA

An Yi Wa Mata 600 Gwajin Cutar Sankarar Mama, An Yi Wa 50 Tiyata A Katsina

An Yi Wa Mata 600 Gwajin Cutar Sankarar Mama, An Yi Wa 50 Tiyata A Katsina

June 15, 2026
Ƴansanda Sun Kashe Ƴan Bindiga Uku Yayin Zazzafar Musayar Wuta

Ƴansanda Sun Kashe Ƴan Bindiga Uku Yayin Zazzafar Musayar Wuta

June 15, 2026
Jamus Ta Sake Yi Wa Abokiyar Karawarta Ruwan Ƙwallaye 7 A Gasar Kofin Duniya

Jamus Ta Sake Yi Wa Abokiyar Karawarta Ruwan Ƙwallaye 7 A Gasar Kofin Duniya

June 14, 2026
Ministoci Da Gwamnoni Za a Koma Kai Wa Hari Nan Gaba – Buratai

Ministoci Da Gwamnoni Za a Koma Kai Wa Hari Nan Gaba – Buratai

June 14, 2026
Jigilar Hajoji Ta Jiragen Kasa Na Gudana Bisa Daidaito A Kasar Sin

Jigilar Hajoji Ta Jiragen Kasa Na Gudana Bisa Daidaito A Kasar Sin

June 14, 2026
Atiku Ya Soki Shirin Bashin Naira Tiriliyan 4 Na Bangaren Wutar Lantarki

Atiku Ya Soki Shirin Bashin Naira Tiriliyan 4 Na Bangaren Wutar Lantarki

June 14, 2026
An Bude Bikin Fina-Finan Kasa Da Kasa Na Shanghai Karo Na 28

An Bude Bikin Fina-Finan Kasa Da Kasa Na Shanghai Karo Na 28

June 14, 2026
Ododo Ya Kai Ziyara Sansanin Horar Dakarun Tsaro Daji A Kogi

Ododo Ya Kai Ziyara Sansanin Horar Dakarun Tsaro Daji A Kogi

June 14, 2026
Jagoran Majalisar Shugabancin Kasar Libya Ya Yi Fatan Ci Gaba Da Ingiza Dangantakar Kasarsa Da Sin

Jagoran Majalisar Shugabancin Kasar Libya Ya Yi Fatan Ci Gaba Da Ingiza Dangantakar Kasarsa Da Sin

June 14, 2026
Sowore Ya Yi Kira Ga Zanga-Zangar Kasa Kan Tinubu Ranar Litinin

Sowore Ya Yi Kira Ga Zanga-Zangar Kasa Kan Tinubu Ranar Litinin

June 14, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.