Rahotanni daga ma’aikatar kula da harkokin kasuwanci ta kasar Sin sun bayyana cewa, tun daga yau 2 ga watan Yuni yarjejeniyar huldar abota ta raya tattalin arzikin shiyyoyi daga dukkan fannoni wato RCEP a takaice ta fara aiki a kasar Philipines a hukumance, lamarin da ya alamta cewa, yarjejeniyar ta fara aiki a kasashe 10 mambobin kungiyar ASEAN da sauran kasashe biyar da suka hada da Australia da kasar Sin da Japan da Koriya ta kudu da kuma New Zealand da suka sa hannu kan yarjejeniyar daga dukkan fannoni.
Ma’aikatar kula da kasuwanci ta kasar Sin ta yi tsokaci cewa, fara aikin da yarjejeniyar RCEP a kasashen 15 ya nuna anniyar wadannan kasashe 15 ta mara baya ga ka’idodijin bude kofa da cinikayya maras shinge da tabbatar da adalci da hakuri da juna, da kuma tsarin cinikayya tsakanin bangarori daban daban.
Ma’aikatar ta kara da cewa, kasar Sin za ta ci gaba da kokarin ingiza aiwatar da yarjejeniyar RCEP yadda ya kamata. (Mai fassarawa: Jamila)