Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi kira da a dauki nauyin gudanar da sabbin ayyukan raya al’adu da gina kasar Sin mai wayewar kai ta zamani.
Xi Jinping wanda kuma shi ne sakatare janar na kwamitin kolin JKS kuma shugaban rundunar sojin kasar, ya yi kiran ne yayin wani taro game da raya al’adun da aka gada da samar da ci gaba, wanda ya gudana a yau Juma’a. (Fa’iza)