Ofishin kula da harkokin zirga-zirgar kumbuna dake dauke da ‘yan sama jannati na kasar Sin ya ba da labarin cewa, ‘yan sama jannati na kumbon Shenzhou-15 sun kammala ayyukansu cikin nasara, sun kuma dawo birnin Beijing a yau da safe.
Bayan da suka iso birnin Beijing, za a kebe ‘yan sama jannatin uku don a binciki lafiyarsu da ba su lokacin hutu, ta yadda za su samu farfadowa. Daga baya, za su zanta da ‘yan jarida a birnin.
A ranar 29 ga watan Nuwamban shekarar 2022 ne, aka harba kumbon Shenzhou-15 daga cibiyar harbar tauraron dan Adam ta Jiuquan, daga bisani ne kuma ya hade da tashar Tianhe a sararin samaniya.
‘Yan sama jannatin 3 sun gudanar da ayyukan nazarin kimiyya da dama, tare da yin tattaki a waje sau 4, matakin da ya aza tubali ga manyan ayyukan kimiyya da fasaha da za a yi a nan gaba. (Amina Xu)